Kasar Sin wata al’umma ce mai wayewar kan dake da dogon tarihi ta fuskar zamani, a matsayin kasa kuma wata hadaddiyar al’ada ce ta gwamnatoci da dama da suka wanzu a lokuta daban-daban. A cikin wannan hadadden tsarin, al’adu da jerin gwamnatoci da yawa ba su yanke alaka da tasiri da juna ba. Sakamakon haka, kasar Sin tsari ne mai sarkakiya na al’adu daban-daban da kuma karfi mai yawa.
Tarihin kasar Sin tarihi ne na dunkulewar kabilu daban daban da hadin kai a kasar, kuma tarihi ne na hadin kan dukkan kabilun kasar Sin wajen samarwa, da raya kasa, da tabbatar da kasa daya mai girma. Tsohuwar kasar Sin ba wata kasa ce da aka ayyana ta hanyar tsarin zamani na kasa-kasa, wanda ke da halaye na “tsararriyar hanyar gudanarwa” ba, sai dai kyakkyawan tsari ne cikin wayewar kai, kuma ba a taba katse ci gaban wayewar kan kasar Sin tun zamanin da zuwa yanzu ba. A yayin da ake ci gaba da samun bunkasuwa, ana kuma ci gaba da inganta wayewar kasar Sin wadda ke yin tasiri ga makobtanta, kuma nasarar ci gaban bude kofa ga waje ya kawo kyakkyawar fata ga makoma da dorewar wayewar kasar Sin har ma da wayewar kan duniya.
- Ra’ayin Kasashe Biyu Da Mahukuntan Taiwan Suka Bayar Ya Shaida Yunkurin ‘Yan Aware Na Taiwan
- Babu Mai Taɓa Sarkin Musulmi – Kashim Shettima
Shugaba Xi ya taba cewa, “al’ada ita ce ruhin kasa da al’umma”. Yankin yammacin kasar Sin yana da dogon tarihi kuma yana da dimbin albarkatun al’adu, kuma ta hanyar kiyaye su yadda ya kamata, da yin amfani da su yadda ya kamata, kasar za ta iya nuna gagarumin karfinta. Kana kwanakin baya, a yayin rangadinsa a lardin Qinghai dake arewa maso yammacin kasar, inda kabilu da dama da suka hadu da ‘yan kabilar Han da sauran kabilu marasa rinjaye ke zama tare, musamman a ziyarar da ya kai wata makarantar sakandare, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin ilimi wajen samar da kyakkyawar fahimtar al’adu da al’umma da wayewar kasar Sin. (Mohammed Yahaya)n