A kwanakin nan ne, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya ziyarci kasashen Cape Verde da Cote d’Ivoire da Nijeriya da kuma Angola, a yunkurin nuna yadda Amurka ke sanya kasashen Afirka a cikin jerin kasashen da take baiwa fifiko a harkokin diplomasiyya. Duk da cewa jami’an gwamnatin Amurka sun yi ta bayyana cewa, ziyarar ba ta da alaka da takarar da take yi da kasar Sin, amma kafofin yada labarai na kasar ta Amurka da dama, suna ci gaba da alakanta ziyarar da batun “dakile tasirin kasashen Sin da Rasha a nahiyar” . Jaridar New York Times a wata makalar da ta wallafa a ranar 22 ga wata, ta bayyana cewa, Afirka nahiya ce da Amurka ke takara da Sin da Rasha, kuma Mista Blinken na “wani kokarin samo wasu kyawawan labarai daga Afirka”.
A hakika, dalilin da ya sa kafofin yada labarai na kasar Amurka suka alakanta ziyarar mista Blinken a Afirka da kasar Sin, shi ne sabo da yadda ’yan siyasar kasar suka dade suna bayyana kasar Sin a matsayin “Babbar dadaddiyar abokiyar takara” a Afirka, wadanda suke ganin cewa, cikin shekaru 20 da suka gabata, tasirin kasar Sin a nahiyar Afirka sai kara karuwa yake yi, don haka, dole ne Amurka ta “dauki matakai na dakile wannan tasiri”.
- Sin Ta Ba Da Rahoton Fadada Shigo Da Kayayyakin Gona Da Na Abinci A Shekarar 2023
- Shirin Cusa Ɗa’a Da Kishin Ƙasa: An Fitar Da Daftarin Yaɗa Kyawawan Ɗabi’un Farfaɗo da Martabar Nijeriya
Wannan ya sa, Amurka a cikin ’yan shekarun baya ta kara daukar matakan siyasa a kan Afirka. Idan ba mu manta ba, a karshen shekarar 2022, Amurka ta kira taron shugabannin Amurka da kasashen Afirka karo na biyu, tsawon shekaru 8 bayan taron da aka gudanar a karo na farko, inda shugaba Joe Biden ya yi alkawarin “yin iyakacin kokarin tabbatar da makomar Afirka”, kuma ya bayyana cewa, zai ziyarci Afirka a shekarar 2023. Amma abin takaici shi ne, shekarar 2023 tuni ta zama tarihi, amma har yanzu shugaban bai ziyarci Afirka ba, kuma ita Amurka din ma ba ta “yi wani kokari na tabbatar da makomar Afirka” kamar yadda ta alkawarta ba, lamarin da ya shaida cewa, Amurka ba ta mai da Afirka a matsayin harkar da take ba wa fifiko ba.
Me ya sa Amurka ke son daukar alkawura a gaban kasashen Afirka amma ba tare da cikawa ba? In mun yi nazari, za mu ga cewa ainihin abin da ya sa take bunkasa alakarta da kasashen Afirka shi ne don su ba ta taimako a ja-in-ja da take da wasu manyan kasashe, a maimakon a ce ta mai da su abokan hadin gwiwa na zaman daidaito da kuma cin moriyar juna, ballantana ta mai da hankali a kan daidaita matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya. Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnatin Biden ta dade tana cewa, za ta yi kokarin bunkasa alakarta da kasashen Afirka, amma kuma ba tare da cimma wani hakikanin sakamako ba. Madam Oge Onubogu,darektar kula da shirin Afirka a cibiyar masana ta kasa da kasa ta Woodrow Wilson da ke birnin Washington na kasar Amurka, ita ma ta bayyana cewa, a ziyarar da ta kai kasashen Afirka, ta gano dimbin manyan ababen more rayuwa da aka samar sakamakon shirin kasar Sin na bunkasa tattalin arziki a kasashen Afirka, amma kasashen Afirka ba su san me kasar Amurka ta iya yi musu ba.
A zahiri dai, bambamcin burin da ake neman cimmawa, ya sa an dauki mabambantan matakai, kuma hakan ya haifar da mabambantan sakamako.
Akasin yadda kasar Amurka ke tsara manufofinta a kan Afirka a yunkurin “yin takara da wasu”, kasar Sin na hulda da kasashen Afirka ne don neman cin moriyar juna, don haka, Sin da kasashen Afirka ke aiwatar da hadin gwiwarsu ta fannin bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma, amma ba tare da tsoma baki a harkokin cikin gidan juna ba, haka kuma ba a gindaya sharudan siyasa ba. Sakamakon hadin gwiwarsu, an gudanar da jerin shirye-shirye na kyautata rayuwar jama’a, kuma manyan ababen more rayuwa na kasashen Afirka ma sun inganta a zahiri. Kafofin yada labarai na kasar Amurka sun kuma lura da cewa, a kasar Cape Verde, Mista Blinken ya sauka ne a wani ginin da kasar Sin ta gina, a yayin ziyararsa a Cote d’Ivoire kuma, ya je kallon gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin kasashen Afirka a filin wasan Alassane Ouattara, wanda kasar Sin ce ta ba da gudummawar gina shi.
A hakika, kullum kasar Sin na ganin cewa, ya kamata nahiyar Afirka ta kasance dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, a maimakon fagen takara a tsakaninsu. Kasashen Afirka yanzu haka na fuskantar kalubale ta fannonin farfadowar tattalin arziki da tabarbarewar harkokin tsaro da sauyin yanayi da makamantansu, don haka, akwai abubuwa da dama da Amurka take iya taimakawa. Kasar Sin na son ganin kasa da kasa sun aiwatar da hadin gwiwar cin moriyar juna bisa daidaito da kasashen Afirka, su samar da taimako na zahiri ga kasashen Afirka a maimakon furta kalaman da ba su dace ba.(Lubabatu Lei)