Mele Kyari, Shugaban Rukunin Kamfanin Mai na NNPCL, ya musanta ikirarin Aliko Dangote na cewa; wasu daga cikin ma’aikatan NNPC na gudanar da wani kamfanin hada-hadar man fetur a Malta.
Dangote ya yi wannan ikirarin ne a wata ganawa da ya yi da ‘yan majalisar wakilai, inda ya bayyana cewa; wasu daga ma’aikatan kamfanin na NNPC da wasu daga cikin dillalan man fetur na da masana’antar hada-hadar man a tsibirin Bahar Rum.
- Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Don Tantancewa
- An Yi Wa Matashi Daurin Rai Da Rai Kan Yi Wa Kurma Fyade A Kebbi
Kyari ya musanta hakan ne a a shafinsa na X (Twitter), inda ya bayyana cewa shi ko wasu daga cikin ma’aikatan NNPC ba wanda ya mallaki ko gudanar hada-hadar da aka zarge su da ita.
Kyari, ya nanata kudurin NNPC na bin bin doka da oda.
Ya bayyana cewa duk wani ma’aikaci da aka samu yana da hannu a irin wadannan ayyuka zai fuskanci hukunci tare da mika shi ga hukuma domin daukar mataki.