Mai karatu a wannan makon zan tabo wasu muhimman abubuwa guda biyu, wadanda ke kishiyantar juna. Kuma dukkaninsu na da alaka da rayuwarmu ta yau da kullum.
A baya hankali na bai taba zuwa kan wadannan abubuwa ba, saboda ko kadan kwakwalwata ba ta sawwalawa ko gabato min da muhimmancinsu da kuma tasirinsu a zamantakewa. Wasu lokuta baya, lokacin muna jami’a, muna darasi, sai malaminmu ya shigo da batun ‘Kyauta da rowa’, ya yi mana dogon bayani (wanda shi a wurinshi ya takaita).
Har ma ya sha alwashin idan Allah ya yarda nan gaba zai yi nazari a kan kyauta da rowa.
Kafin na ci gaba da bayani, akwai wani abu mai sarkakiya wanda ya kamata mu warware shi. Shin kyauta ko rowa a na yin gadonsu ne, ko kuwa koyonsu a ke yi?
Wannan tambayar ba ta da wani bambanci da tsohuwar tattaunawar nan dangane da dabi’ar dan Adam, wanda wasu ke hakikancewa a kan cewa ai dabi’a ta na tattare ne a cikin jininmu, daya bangaren kuma suka ce, a na koyon dabi’u ne a cikin al’umma.
Idan mutum na da yawan kyauta, za ka ji hausawa na cewa ya na da jinin kyauta. Sai dai wannan karin magana kadai bai isa ya zama madogara gare mu ba, ballantana har mu yanke hukuncin cewa ai in dai mutum ya hada jini da masu kyauta babu makawa shi ma zai zamo mai kyauta.
Wannan rusasshen zance ne, idan za mu yi la’akari da dan kwatance kamar haka; misali akwai tagwaye (twins) wadanda a ka haifa a garin Kaduna. Sunansu Hasan da Husaini, tun bayan kwana bakwai da haihuwansu, sai mahaifinsu ya yanke shawarar zai raba su wurare daban daban a hannun kannenshi.
Da aka tashi sai a ka kai Hasan kasar Ingila, shi kuma Hussaini a ka kai shi garin Gombe. Har zuwa lokacin da su ka girma su ka fara aiki.
Abun lura a nan shi ne, idan Hasan da ke kasar ingila ya taso tare da mutane masu ra’ayin turawa na cewa taimakon talaka kuskure ne, saboda idan yau ka taimaki talaka ba zai mike ya nemi na kanshi ba. Shi kuma Husainin ya taso a wurin mutanen Gombe, wadanda za su iya sadaukar da dukkan abun da ke cikin aljihunsu domin yin hidima ga bako, ko kuma mutanen da ke fito da abinci kofar gida a taru a ci.
Wannan ya nuna mana a fili cewa Hasan zai koyo rowa matsananciya, shi kuma Husaini zai koyo yadda a ke kyautata ma mutane. Wannan dan gajeren misali kadai ya isa mu gane karfin ikon wurin da mutum ya taso ga halayyenshi, musamman halin kyauta ko rowa.
Tun a rayuwarmu ta yau da kullum mu kan ga alheran da ke tattare da kyauta, haka kuma mu kan ga sharrrukan da ke tattare da rowa. Mutumin da ke da kyauta, ya kan zama mafi soyuwa a tsakanin mutane, sannan mutane ba za su aminta a hada kai da su wurin cutar da shi ba.
Akasin haka ga marowaci. Idan mai gida (oga) ya kasance marowaci, babu makawa da yaranshi (ma’aikata) za a hada baki a halaka shi ko a gurgunta al’amuranshi. Saboda ai tsaro ba ya na nufin mai gadi da bindiga ba ne kawai, mafi girman tsaro shi ne tsaro wanda mutum ya samarwa kanshi ta hanyar mallakar zukatan wadanda ya ke tare da su.
Idan kai mai arziki ne, amma ma’aikatanka ko da yaushe su na cikin matsanancin wahala. Kenan watan wata rana makiya za su iya ba mai dafa mishi abinci (kuku) guba ya zuba mishi don ya ci ya halaka.
Sirrin cin moriyar rayuwa na tattare da kyauta. A wasu lokutan ma kyautar da mutane ke yi kanana su na ganinsu ba a bakin komi ba, amma wannan abun alheri zai ci gaba da binsu har ‘ya ‘ya da jikoki.
Idan kuwa halin ka kenan rowan tsiya, wannan tabon na marowaci, ya yi ta binka kenan. Har ma idan a ka ci sa’a cikin ‘ya ‘yanka ko jikoki a ka samu wani mai halin kyauta, sai ka ji jama’a na cewa Allah sarki mahaifinshi ko Kakanshi marowaci, amma shi kuma mai kyauta.
Abubuwa biyu ne masu karo da juna. Sai dai yana da kyau mu gane cewa wadannan halaye guda biyu, al’umma na da hakkin koya wa mutum su. Idan muka kasance masu halin kyautatawa, ‘ya ‘yanmu da wadanda ke tare da mu za su taso da wannan hali. Shi ya sa masana a kimiyyar zamantakewa suke cewa al’umma ne ke gina dabi’ar mutum.
Mu hadu a mako mai zuwa