A yau Talata ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar Kasar Sin, inda firaministan kasar, Li Qiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati a bara. Cikin rahoton ya bayyana cewa, “Gwamnati ta cimma nasarar samun ci gaba mai inganci, da tabbatar da zaman lafiyar al’umma, lamarin da ya sa aka sami gagarumin ci gaba a fannin gina zamantakewar al’umma ta zamani bisa tsarin gurguzu a dukkanin fannoni.”
Dukkan ci gaban kasar Sin baya rasa nasaba da irin tsarin shugabancin da ta zabarwa kanta. Tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, shi ne tushe kuma sirrin ci gaban kasar. Sin ta yi abun da ba kasafai a kan gani ba, wato ta duba yanayinta, ta kuma fadawa kan ta gaskiya, inda ta rika aiwatar da manufofi da dabarun da suka dace da yanayinta, maimakon zama ’yar a bi Yarima a sha kida.
Na saba da jin ana cewa, “in dambu ya yi yawa baya jin mai” wato idan mutane suka yi yawa, to da wuya kowa ya ci gajiyar wata manufa ko shirin kyautatawa al’umma. Sai dai, zan iya cewa, duk da dimbin jama’a da kasar Sin take da shi, ba na jin ana irin wannan furuci, har kullum manufofin kasar kan isa ga wadanda aka yi domin su.
Wani batu shi ne, Kishin Kasa. Ana yawaita samun rikicin addini ko kabilanci a cikin gidan kasashen duniya da dama, amma duk da yawan kabilu da addinai dake a kasar Sin, ba ka jin tashin irin wadannan rigingimu. Abun da na lura da shi da al’ummar kasar shi ne, duk da cewa akwai kabilu daban daban, tuna cewa kai Basine ne, shi ne abu na farko kuma mafi muhimmanci kafin komai. Wato an dasawa Sinawa kishin kasa da kaunar kasa kafin komai, wanda ya zama tushen zaman lafiya da zaman jituwa da hakuri da juna da ake samu tsakanin al’ummun kasar daga mabambantan kabilu.
Jawabin nasa ya kuma tabo ci gaban da aka samu a bangarorin tattalin arziki da fasahohi da kirkire kirkire, amma na mayar da hankali ne kan yanayin zaman takewar jama’a da irin ci gaban da suke samu, saboda yadda hakan ke ja hankalina matuka, kuma saboda ina kwadayin ganin an samu irin hakan a kasata da sauran sassan duniya. Duk wani yunkuri ko manufa da kasa za ta aiwatar, ba za su taba yin tasiri ba idan babu jama’a. Haka ma, duk burin samun ci gaban da take da shi, ba za ta iya cimmawa ba, muddun al’ummarta na cikin kuncin rayuwa ko rikici da juna.
A matsayin wadda ta shaida yanayin rayuwar Sinawa, tabbas zan iya cewa ci gaban kasar ya samo asali ne daga yadda ta mayar da hankali kan raya jama’arta da kyautata rayuwarsu da tabbatar da daidaito da girmama juna tsakanin mabanbantan kabilu.