A bana ake cika shekaru 70 da kafuwar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, shin wadanne sauye-sauye ne suka faru a jihar cikin shekarun 70 da suka gabata. Jama’a, ku biyo mu a zauren “Labaran Xinjiang a zane,” inda za mu gabatar muku jerin zane-zane don fahimtar sauye-sauyen da suka faru!
A yau, za mu gutsura muku labarin yadda hamada ta zama gonaki a jihar ta Xinjiang.
Fiye da kashi 60% na filayen Xinjiang hamada ne. Duk da haka, cikin sama da shekaru 10 da suka wuce, fadin gonakin hatsi ya karu da muraba’in kilomita 8000 a jihar, ko ta yaya aka cimma wannan nasara?
Li Wenbin, dan gundumar Qiemo ne, wadda ke cikin hamadar Taklimakan a kudancin jihar Xinjiang, ya bayyana cewa, babban kalubalen da ake fuskanta wajen noman amfanin gona a hamada shi ne ban ruwa, don haka, bai taba yin zaton noman hatsi a cikin hamada ba. Amma nesa ta zo kusa ne sakamakon kafuwar madatsar ruwa ta Dashimen, matakin da ya sa abun da a baya bai yiwu ba a yanzu ya kasance mai yiwuwa.
Madatsar ruwa ta Dashimen, daya ce daga manyan ayyukan ban ruwa 172 na kasar Sin, kuma tana gundumar Qiemo. An fara gina ta ne a watan Oktoban shekarar 2015, kana an fara adana ruwa cikinta tun watan Satumban shekarar 2021. Bisa tsarin wannan madatsar ruwa, an kai ga janyo ruwan dusar kankara daga tsaunin Kunlun, mai nisan daruruwan kilomita, har zuwa hamadar. Hakan ya sa babu wata matsala dake damun Li Wenbin, har ya yi nasarar shuka alkama, da masara, dankalin Turawa, da sauran amfanin gona a cikin hamada.
Ba madatsar ruwa ta Dashimen kadai ce ta ba da damar noma amfanin gona a cikin yankin hamada ba. A cikin shekaru goma da suka gabata, yawan madatsan ruwa da aka gina ko gyara a yankin kwarin Tarim ya kai fiye da 120, wadanda suka hada rassan kogin Tarim 144, kuma hakan ya samar da babban tsarin ban ruwa a wurin, har ya mai da sassan hamada su zama gonaki.
A cikin hamadar da ke gundumar Qiemo, ana ta kara samun dausayi, inda masarar da malam Li Wenbin ya shuka ta kusan nuna. A cikin shekaru goma da suka gabata, karuwar gonaki a jihar Xinjiang ta kai fiye da muraba’in kilomita 8000, wanda ya sa jihar zamanto yankin da ya fi yawan karuwar hatsi a kasar Sin, kuma mazauna jihar Xinjiang irinsu Li Wenbin, suna jin dadin rayuwarsu duba da girbi mai armashi da suke yi a gonakinsu. (Mai zane da rubutu: MINA).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp