Masu hikimar magana sun ce: kifin zinare ba shi da wurin buya. Wanda a lokuta da dama irin wannan, a samu jajirtaccen mutum mai irin wannan siffar kifin zinariyar; mafi akasari ya na zuwa ne bayan tsallake ma’aunan tantancewa guda uku, fannin ilimi, dukiya da shugabanci, wanda daga bisani hakikanin sa ya bayyana.
Ta hanyar la’akari da Hon. Mai Mala Buni, a matsayin sa na zababben gwamnan jihar Yobe na hudu, a jerin Gwamnonin da jihar Yobe tayi tun bayan komowa tafarkin dimokuradiyya, baya ga shafe shekaru 30 yana gudanar da rayuwa mai tasiri, kama daga matakin karamar hukumar sa, jihohi, da kasa baki daya, yayin da kowane taki na wannan doguwar tafiya a yau wata alama ce ta nasara a sama, tare da fuskantar manyan kalubalen da nasara ta zama cika-makin su.
Ga wani mutum wanda Allah ya albarkace shi da hali na tawali’u, tausayi, samun dama, tare da hazaka kana mai kawaici wajen barin abin da ya dace kuma halal, domin samun zaman lafiya da maslaha.
Wadannan kyawawan dabi’u sun bayyana ga wannan hazikin Shugaba, tun yana karami, a lokacin da yake dalibin Sakandare, cike da shaukin kuruciya, ya bai wa yan uwansa da kawunsa, da sauran al’ummar Buni-Gari, ya bayar da mamaki a lokacin da ya sadaukar da gadonsa da ya mallaka ga sauran yan uwansa, domin hadin kai da maslaha a zamantakewar iyali. Wannan karamci ne wanda ba kasafai ake samunsa ba, face sai a wajen mutane na musamman a cikin al’umma.
Wanda a cikin kwazo da himma, daga bisani, Mai Mala Buni, ya fara a matsayin dan kasuwa (sana’ar hatsi da karo).
An haife Mai Mala Buni a ranar 19 ga Nuwamban 1967, kuma ya samu cikakkiyar kulawar mahaifin shi, wanda sanannen attajiri ne a lokacin da yake karatun sakandare, wanda hakan ya zame masa turba tagari wajen kasancewa abin sha’awa ga kowa, ta hanyar karimcinsa da halayensa nagari tare da jawo masa tagomashin abokanai wadanda har yanzu suna tare dashi a matsayin aminai.
Bayan kammala karatunsa na Sakandare, bisa la’akari da bukatar jama’a, al’ummar gundumar Buni-Gari suka bukaci Hon. Mai Mala Buni ya wakilce su a matsayin Kansila a karamar hukumar Gujba, wanda daga bisani kuma ya zama shugaban kansiloli (Speaker), karamar hukumar Gujba a 1991-1992. Kuma a matsayinsa na shugaban majalisar, yana da gagarumin rinjaye wanda hakan ya bashi damar zama shugaban kansiloli mafi karfin fada aji a tsohuwar jihar Borno.
Gwamna Buni ya rike mukamin Mataimaki a Majalisar kasa a 2000 da kuma a 2004, an nada shi a matsayin mamban gudanarwa a Jami’ar Uyo, yayin da daga bisani aka zabe shi a matsayin Shugaban Advanced Congress of Democrats (ACD) na jihar, kana kuma Shugaban jam’iyyar Action Congress (ACN) tsakanin 2006 zuwa 2010.
Tauraruwarsa ta siyasa ta ci gaba da haskakawa, musamman a lokacin da aka nada shi babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Yobe kan harkokin jam’iyyu, 2009 zuwa 2011.
Wanda bayan zaben 2011, Sanata Ibrahim Gaidam ya Hon. Mai Mala Buni mai bashi shawara na musamman kan harkokin siyasa da Majalisar dokoki, mukamin da ya rike har zuwa shekarar 2013 lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban sabuwar jam’iyyar APC na jihar Yobe.
Jirgin siyasar Mai Mala Buni cilla a sararin samaniya, yayin da aka zabe shi a matsayin babban sakataren jam’iyyar APC na kasa wanda ya bashi dama wajen saita da dama daga cikin manyan kalubale da rigingimun da jam’iyyar ta sha fama dasu a kasa baki daya.
Gudunmawar da ya bayar wajen sake fasalin dimokuradiyyar Nijeriya yayi armashi a zahiri saboda a lokacin sa ne sabuwar jam’iyyar adawa ta APC ta kori jam’iyyar PDP daga kan karagar mulki a lokacin shugabanta Goodluck Jonathan, inda ta lashe zaben 2015 wanda ya kawo Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa.
A lokacin da yake wa’adinsa na biyu a matsayin sakataren jam’iyyar APC na kasa, masu ruwa da tsaki a jihar Yobe baki daya suka tsayar da shi a matsayin wanda suke so ya tsaya takarar gwamnan jihar, wanda hakan ya kara tabbatar da karin maganar nan da ke cewa “kifin zinari ba shi da maboya.”
An zabi Buni ne da gagarumin rinjaye, kuma karbuwar sakamakon zaben ya yanke rarrabuwar kan jam’iyyun siyasa, kabilanci da na addini a fadin jihar Yobe.
Al’amarin da ya kai ga hatta jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna a jihar Yobe, Amb. Umar Iliya Damagum, bisa ra’in ransa ya fito fili ya bayyana cewa ba zai kalubalanci nasarar da Gwamna Buni ya samu ba, kuma ba zai je kotu ba. Inda ya mika hannun yan jam’iyyar PDP domin su shiga gwamnatin a gina jihar Yobe.
Ta la’akari da tarin ilimi da gogewar siyasa da mulki da Hon. Buni yake dasu, wanda bayan wasu rigingimun da uwar jam’iyyar APC mai mulki ta fuskanta a 2020, kwamitin zartaswar jam’iyyar na kasa ya bukaci mutum mai natsuwa, mai taushin hali, mai in ra’ayin da halayen maslaha da sulhu- shi ne ta bukace shi ya zo don ya cetota, wanda ta jawo ta nada Gwamna Buni a matsayin Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Musamman na Rikon Jam’iyyar APC.
A wannan karon ne ‘kifin zinariya’ ya sake fitar da siffarsa a fili, a lokacin da ya hada ofisoshi biyu na Gwamna da shugaban riko na jam’iyyar APC a tsawon watanni 21. Wanda a cikin tsanaki da kwanciyar hankali ya raba gardama. Kuma wadannan kyawawan halaye nasa sun bashi damar shiga tsakani, a matsayin sa na limamin sulhu kuma mai son zaman lafiya, ya sadaukar da kansa wajen aikin yiwa kasa hidima.
A lokacin sa ne gwamnoni uku a jihohin Cross Riber, Ebonyi, da Zamfara suka sauya sheka daga PDP zuwa APC tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka kauro zuwa APC.
Aikin yiwa kasarsa hidima bai hana Gwamna Buni aiwatar da muhimman ayyukan raya jihar Yobe ba:
A lokacin da ya hau kujerar Gwamna a ranar 29 ga Mayu, 2019, Gwamna Buni ya ayyana dokar ta-baci kan ilimi tare da yin alkawarin kafa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda daya gundumomi 178 da ke fadin jihar Yobe, inganta ayyukan noma, matasa da mata don samun dorewar hanyoyin rayuwa da bunkasa ababen more rayuwa, a matsayin jerin abubuwan da gwamnatins zata sa a gaba.
A cikin taimakon Allah, an kammala cibiyoyi 138 daga cikin 178 wanda ya alkawarta, tare da mayar da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda shida zuwa manyan asibitoci kana kuma an daga darajar wasu manyan asibitoci hudu zuwa na kwararru. An inganta kayan aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar jihar Yobe don dacewa da sauyin yanayi, wanda hakan ya sa asibitin koyarwa ya zama mafi kyau a fadin kasar nan wadda aka saka kawatata da na’urorin da ake alfahari dasu na zamani.
Jihar Yobe a yau tana kula da majinyata kamar kowace kasa a fadinn duniya kuma tana ci gaba da kasancewa a matsayin mai jan hankali tare da sha’awa ga kwararrun likitoci saboda kayan aiki masu ingancin da suke shaukin aiki dasu.
Alh. Adamu Hashimu, babban sakatare na dindindin daga jihar Bauchil ya shaida hakan, wanda ya taba kai dansa jinya a kasar Masar domin yi masa tiyata amma daga bisani aka dawo dashi Asibitin Koyarwa na Jami’ar jihar Yobe tare da tabbatar da abin da jihar Yobe ke alamta a fannin likitanci.
Wani Likitan makwabcinsa ya ba shi shawarar ya je Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe a kan jinya a kasashen waje. Kuma an yi wa dansa tiyata na farko a kasa da Naira 40,000.
Ya bayyana cewa “Ban taba tsammanin za a iya samun makamancin wannan Asibiti ba a nan jihar Yobe, Gwamna Mai Mala Buni ya yi kokari na musamman wajen kawo wa al’ummarsa ayyukan kiwon lafiya mai sauki da inganci.”
Ya bayyana cewa gwamnatin Yobe a karkashin Gwamna Buni, ita ce jiha ta farko a shiyyar Arewa maso Gabas da ta bullo da shirin bayar da gudunmawar kiwon lafiya da aka fi sani da Yobe State Contributory Health Management Agency (YOCHMA) da Yobe State Drug Management Agency (YODMA) domin samar da isassun kudade da samar da magunguna ga majinyata a karkashin shirin gwamnatin jiha na fadada magunguna kyauta wanda ya shafi mata masu juna biyu, yara, wadanda hatsarin mota ya rutsa da su, masu rauni da tsofaffi, da sauran mutane masu rauni. A halin yanzu, akwai sama da masu cin gajiyar shirin kimanin 400,000 a Yobe. Kuma an fadada shirin don cike gibin da iyalai masu karamin karfi ko marasa galihu.
Har wala yau kuma, domin bunkasa ma’aikatan lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya, sama da likitoci 30, wadanda suka kammala karatun jinya a kwalejin horas da ma’aikatan jinya da ungozoma mallakin gwamnatin jihar, da kuma 50 da suka kammala Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya, da makamantan su domin bunkasa Harkokin kiwon lafiya.
Wannan ya tabbaar da cewa Gwamnatin Buni ta tsunduma wajen bunkasa kiwon lafiya tare da biyan hakikanin su kan kari ta hanyar samar da hanyoyin kiwon lafiya da araha ga jama’a. Kuma ba abin mamaki bane jihar Yobe ta zama cibiya da jan hankalin marasa lafiya daga jihohin da ke makwabtaka a fannin kawo majinyatansu a jihar.
Shigar Jihar Yobe a harkokin kiwon lafiya na kasa abin koyi ne, wannan ya bayyana irin kwazon da jihar ta yi wajen gudanar da alluran rigakafi na kasa wanda ya kai ga samun lambar yabo ta jihar da ta fi kowa aiki.
Gwamnatin Buni ta gyara makarantun tare da gina karin wasu makarantu shida na zamani hadi da Mega School bakwai don rage cinkoson dalibai, sayan litattafai da kayan aikin dakin gwaje-gwaje, kara adadin yawan malamai da basu horo da karin girma ga daruruwan malamai domin inganta ilimi da walwalar ma’aikatan jihar. Haka kuma gwamnati na daukar nauyin dalibai da dama da ke karatu a wasu kasashe a fadin duniya.
Bugu da kari kuma, Gwamna Buni ya kammala filin jirgin saman kasa-da-kasa na Cargo mallakar jihar. Wanda yanzu yana shirye don kaddamarwa. Har ila yau, ya kaddamar da gina kasuwannin zamani guda hudu a manyan buranen jihar domin samar da yanayi mai kyau na kasuwanci don bunkasa tattalin arziki, kana ya farfado da masana’antu guda uku da suka kwanta dama, da samar da ayyukan karfafawa mata da matasa sana’o’in dogaro da kai, da gina gidaje 1,800 mafi girma tun bayan kafa jihar.
Gwamnatin Buni ta gina titunan a garuruwa da dama don saukaka zirga-zirgar kayayyaki da na jama’a. Gwamnati ta kuma samarwa al’ummomi 133 wutar lantarki don inganta rayuwa ga al’ummar.
A yau, an sami karuwar sana’o’in dogaro da kai da karfafa tattalin arziki a cikin al’ummomin da ke amfana.
A karkashin ingantaccen jagorancin Gwamna Buni na sauya harkar noma zuwa na zamani domin bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fadin jihar Yobe. Sannan wani abin farin ciki shi ne irin yadda masu sa ido kan kasafin kudi na masu zaman kansu suka ayyana gwamnatin Buni a matsayin wacce ta fi kowace jihar a Nijeriya wajen aiwatar da kasafin kudi, tare da biyan albashin ma’aikata.
“Wadannan su ne ginshikan da suka kai ga Gwamna Mai Mala Buni ya samun manyan nasarori a rayuwarsa, kuma ba abin mamaki ba ne a iya ganinsa kewaye da dimbin lambobin yabo na karramawa; wanda a wannan gabar ya karbi yabo mafi tsada na girmamawa ta kasa, ta Commander of the Order of the Nigeria, CON.