Hukumar kwastam na lardin Hainan na kasar Sin, ta fitar da wani rahoto dake cewa, lardin ya samu karuwar cinikayyar hajoji da aka daukewa haraji cikin shekaru biyar da suka gabata, tun bayan fara aiwatar da manufar fadada damar sayayyar kayayyakin da aka daukewa haraji.
Adadin kudaden hajojin da aka sayar karkashin tsarin cikin shekarun biyar, ya kai kudin Sin yuan biliyan 195.8, kimanin dalar Amurka biliyan 27.4. Kazalika, cikin wa’adin na shekaru biyar, adadin masu sayayya da suka sai hajoji a lardin sun kai kusan miliyan 28.59.
Tun a watan Yunin shekarar 2020 ne kasar Sin ta fitar da wani tsari na mayar da lardin Hainan wata cibiyar duniya mai tasirin gaske, a fannin cinikayya marar shinge bisa matsayin koli, zuwa tsakiyar karnin nan da muke ciki.
Kazalika, kasar Sin na fatan mayar da Hainan babbar cibiyar kasa da kasa ta yawon bude ido da sayayya nan zuwa shekarar 2035. A ‘yan shekarun baya-bayan nan, tsibirin na Hainan ya zamo wuri mai matukar jan hankalin masu sayayyar kayayyaki na cikin gida. (Saminu Alhassan)













