Lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, ya samu tagomashin cinikayyar waje tsakanin sa da kasashen nahiyar Afirka, cikin watanni 3 na farkon shekarar nan, inda darajar cinikayyar bangarorin 2 ta kai kudin Sin yuan biliyan 14.47, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2, kamar dai yadda alkaluman hukumar kwastam ta birnin Changsha, fadar mulkin lardin na Hunan suka bayyana.
Wadannan alkaluma dai sun nuna karuwar kaso 82.9 bisa dari a shekara, a gabar da lardin na Hunan ke kasancewa wuri mafi dadewa yana karbar bakuncin baje kolin harkokin cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka. A bana ma, baje kolin na Hunan zai gudana ne a watan Yuni, inda ake sa ran zai kara ingiza ci gaban alakar cinikayya tsakanin sassan 2.
Alkaluman kwastam din sun nuna cewa, a rubu’in farko na bana, lardin Hunan ya fitar da hajoji zuwa Afirka da darajar su ta kai yuan biliyan 11.19, adadin da ya nuna karuwar kaso 131.2 bisa dari a shekara, kana ya shigo da hajojin da darajar su ta kai yuan biliyan 3.28, adadin da ya shaida karuwar kaso 6.8 bisa dari a shekara.
Kamfanoni masu zaman kan su sun taka rawar gani a fannin ingiza cinikayyar waje. Kuma lardin Hunan na fitar da galibin hajojin da suka shafi na’urorin masana’antu da na latironi, da na samar da manyan hidimomin sarrafa hajoji, da karafa, yayin da kuma yake shigo da albarkatun karfe da gangar ruwa. (Saminu Alhassan)