Lardunan kasar Sin guda 8, sun samu karuwar GDP da kaso sama da 5 bisa dari, a rubu’in farko na shekarar nan ta 2023.
Rahotannin da gwamnatocin lardunan 8, cikin jimillar larduna 20 na kasar suka fitar, sun nuna yadda lardin Jilin ke kan gaba da karuwar kaso 8.2 bisa dari na karfin tattalin arzikin sa, sai kuma lardin Ningxia da ya samu karuwar kaso 7.5 bisa dari, yayin da lardin Hainan ya samu karuwar kaso 6.8 bisa dari.
Bisa jimilla, kasar Sin ta samu karuwar kaso 4.5 bisa dari na GDPn ta cikin watanni ukun farko na bana. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp