Masu karatu assalamu alaikum. Barkan mu da kara saduwa a wannan makon a cikin filinku mai farin jini na Ado da Kwalliya.
Idan ba a manta ba, tun a makonni uku da suka gabata muna bayani ne a kan launukan da za a kawata falo da su masu ban sha’awa.
- Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azama Kan Masana’antu Wajen Yin Kirkire-kirkire
- An Shirya Tattaunawar Tiangong Tsakanin ‘Yan Sama Jannatin Sin Da Matasan Afirka Cikin Nasara
A yau ma filin zai ci gaba da wannan batu. Inda cikin yardar Allah za mu kammala a wannan makon. Ga ci gaban bayanin: Ruwan Hoda (Pink) Launin ruwan hoda yana daga cikin launukan da ke kayatarwa mai ban mamaki idan aka yi amfani da shi wurin kawata adon falo.
Launi ne da ke bukatar tsari mai kyau ta yadda ido ba zai gaji da kallonsa ba. Shi ma idan aka ratsa masa wasu kaloli da suka dace da shi ya fi kayatarwa.
Kalolin da za su yi kyau da tsari tare da ruwan hoda sun hada da fari, ruwan madara da ruwan toka musamman mai haske da sauransu.
Ruwan Kirim (Cream)
Wannan launin yana da matukar farin jini a wurin mutane da yawa wajen kawata falo. Watakila ya samu wannan tagomashin ne saboda yadda ya zama na daban a cikin sauran launuka.
Ruwan Kirim ba ya bukatar a rage masa duhu ko kara masa haske, watakila shi ya sa idan za ki sa a yi amfani da shi a falo ba ki da bukatar sai dole kin hada shi da wani kebantaccen launi sannan ya ba ki abin da kike so.
Shi yana iya dacewa da kowane a cikin duk kalolin da kike da sha’awar hada su.
Ruwan Kwai ko Tsanwa (Yellow)
Launi ne da yake cikin manyan launuka guda goma da aka fi amfani da su wajen kawata falo, kuma shi ma ana iya yi masa kirari da “kanwa uwar gami”.
Idan aka hada shi da kore yana ba da ma’ana sosai tun ma ba an kara kawata falon da kujeru da darduma na asali ba.
Duka-duka abin da ya sauwaka mana kenan a kan wannan batu na Kalolin da ake kawata falo da su masu ban sha’awa.
Idan Allah ya kai mu mako mai zuwa, za mu kawo muku sabuwar tsaraba. Mu tara da yardar Mai Duka.
Mun samo daga: https://www.countrylibing.com/uk/