An maka shahararrun mawakan zamani da fitattun ma’abotan shafin sada zumunta na TikTok a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke garin Bichi a Jihar Kano bisa zargin lalata tarbiyya a tsakanin al’umma.
Majiyoyi sun ce laifuffukan sun hada da wakokin rashin tarbiyya da rawar Tiktok da ke da alaka da lalata tarbiyyar al’umma.
- 2023: Ba Da Jimawa Ba Za Mu Wallafa Cikakken Sunayen Wadanda Aka Yi Wa Rajistar Katin Zabe – INEC
- An Kama Mai Shiga Tsakanin Iyalai Da Masu Garkuwar Jirgin Kasan Kaduna A Masar
Sai dai LEADERSHIP Hausa, ta samu kwafin wasikar da kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa ‘yan sanda na neman a binciki koke-koken da ke gaban masu gabatar da kara.
Wadanda aka zayyana a wasikar da aka aika wa kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano sun hada da Mista 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Murja Ibrahim Kunya, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiyana.
“Sakamakon karar da Muhd Ali Hamza Esq, Abba Mahmud, Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B.I Usman Esq, Muhd Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi & Badamasi Suleiman Gandu Esq su ka gabatar.
“Alkali mai shari’a na Babbar Kotun Shari’a na Bichi a Kano ya umurce ni da in rubuta tare da neman ku da ku gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin a sama domin daukar matakin da ya dace.
“An makala kwafin takardar korafin don ƙarin bayani. Ka huta lafiya,” in ji wasikar, wacce rijistaran kotun, Aminu Muhd ya sanya wa hannu.