Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin da Faransa na da mahanga daya a muhimman fannonin ci gaba, a matsayin su na mambobin dindindin cikin jimillar kasashe masu kujerun dindindin 5 a kwamitin tsaron MDD. Li Qiang ya yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamis, yayin da yake zantawa da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris.
Da yake mayar da martani ga kalaman na Li Qiang, shugaba Macron ya ce kamata ya yi kasashen 2 su rungumi akidar cimma moriyar cudanyar sassa daban daban, da bunkasa goyon bayan juna tsakanin sassan kasa da kasa.
A wani ci gaban kuma, Li Qiang ya zanta da firaministar Faransa Elisabeth Borne. Yayin tattaunawar ta su, Li ya ce Sin za ta yi aiki tare da Faransa wajen bunkasa fannin kasuwanci, da tabbatar da cimma moriyar juna tsakanin kasashen biyu.
Kaza lika yayin da yake zantawa da shugaban majalissar Turai Charles Michel, a gefen taron nazarin sabuwar yarjejeniyar samar da kudaden gudanar da ayyuka ta kasa da kasa, firaministan na Sin ya ce ci gaban kasar Sin, ya samar wa daukacin duniya damammaki, ba wai hadurra ba.
Li ya kara da cewa, bunkasar kasar Sin na haifar da daidaito ba wai matsaloli ga tsarin sarrafawa, da rarraba kayayyaki masana’antu ba.
Daga nan sai ya yi fatan cewa, kungiyar tarayyar Turai ta EU, za ta rika kallon hadin gwiwar ta da kasar Sin bisa adalci, ta kuma yi aiki tare da Sin din wajen samar da kyakkyawan yanayin bunkasa hadin gwiwar sassan biyu yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)