Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewar Aiki (NARD) reshen Babban Birnin Tarayya (FCT) ta fara yajin aikin gargaɗi na tsawon kwana bakwai a yau Litinin.
Sanarwar da shugaban ƙungiyar, Dakta George Ebong tare da wasu shugabannin ƙungiyar suka sanya wa hannu, ta bayyana cewa matakin ya zama dole saboda matsalolin tsarin lafiya da suka daɗe suna addabar FCT.
- FCTA Ta Rufe Hedikwatar PDP Ta Ƙasa Saboda Ƙin Biyan Harajin Ƙasa
- 2027: Idan Kana Son Tarwatsa PDP, To Ka Dawo Da Peter Obi – Wike
Ƙungiyar ta ce tsarin kiwon lafiya a Abuja na fama da matsaloli masu zurfi da suka daɗe ba a warware su ba, tana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa na gyara.
Ebong ya jaddada cewa Likitoci masu neman ƙwarewar aiki a FCT suna cikin matsin lamba sosai, inda ake tilasta musu jagorantar sassa da dama lokaci guda, abin da ke haifar da gajiya da rage gudanar da aiki ingantacce.
Ƙungiyar ta ce yajin aikin gargaɗi ne kawai, amma ta yi gargaɗin cewa za a tsawaita shi idan gwamnati ta kasa ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp