Wani dan kasar Tanzania da ya je asibiti da korafin diwa na yawan fita daga cikin nononsa na dama, ya shiga cikin dimuwa da gigicewa yayin da ya fahimci yana rayuwa da wani katon wuka a cikin kirjinsa ba tare da ya sani ba na tsawon shekaru har takwas, kafar yada labarai ta kasar ce ta rawaito.
Likitoci a babban asibitin Muhimbili da ke Tanzania a baya-bayan nan suka wallafa rahoton wani jinya wanda ba a saba samun irinsa ba, wanda ya zo da ban mamaki matuka.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Sanata Wadada Ya Fice Daga Jam’iyyar SDP Bayan Ganawa Da Tinubu
Sun rubuta cewa, wani mutum dan shekara 44 a duniya da ke cikin rayuwa da koshin lafiyarsa, ya kawo musu korafin cewa cikin kwanaki goma yana ganin farin ruwan diwa na fita daga nononsa na dama.
Sai dai ya ce shi baya jin wani zafi a cikin kirjinsa, ko wahalar jan numfashi, tari ko zazzabi, da aka tambaye shi ko yana da wani abu na daman da zai iya fada wa likitocin, sai ya tuna cewar a shekaru takwas da suka wuce sun taba yin fada, wanda a lokacin ya samu yanka (raunuka) a fuskantasa, kirji da kuma cikinsa.
Ya tabbatar da cewa tun a can lokacin likitoci sun dinke ramuka da raunukan da ya samu kuma ya ci gaba da rayuwarsa samul-garau, har sai lokacin da nononsa ya fara fitar da farin ruwa na diwa.
Bayan da likitocin suka kasa gane wacce irin cuta ce take janyo masa wannan fitar da diwan, likitocin sun umarci a je a dauki hoton kirjinsa, inda a nan ne suka gano katoton wukan da aka burma a cikin mutumin.
Likitocin sun rubuta cikin rahoton binciken nasu cewa hoton farko da aka dauka ya nuna zanen wani abu da ke kwance cikin kirjin mutumin, wanda daga bisani aka gano balo-balo wuka ne.
Sai dai sun gano cewa wukan tun lokacin da aka burma shi bai zaga ko lalata wasu sassan gabobin mutumin ba.
A lokacin da aka sanya masa wukar shekaru takwas da suka wuce, asibitin da suka masa dinkin, ba su ga wani alami ko dalilin da zai sanya su zurfafa bincike ba saboda bai musu korafin jin wani zafi ba, illa ya nuna garau yake ji, don haka a wancan lokacin babu bukatar zurfafa bincike, a cewar rahoton.
Sai dai rahoton ya nuna mamakin yadda mutumin dan shekara 44 ya ci gaba da rayuwarsa ba tare da wata matsala ba, duk kuwa da cewa diwan ya fito ne sakamakon matattun nama da suka kewaye jikin wukar.
Bayan gano wukar a kirjin mutumin, likitocin sun yi tiyata tare da ciro wukar da sauran naman da suka lalace da fitar da diwan baki daya.
Majinyacin ya kwashe awanni 24 a sashin kulawa ta musamman kafin daga bisani aka maida shi zuwa dakin jinya na tsawon kwanaki goma. Ya samu lafiya sosai ya kuma ci gaba da rayuwarsa ba tare da jin wani zafi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp