Kungiyar Likitocin Nijeriya reshen Jihar Kaduna, ta yi jan hankali game da cututtuka masu saurin yaduwa kamar su cutar kyandar biri, Ebola da kuma zazzabin Lassa a Nijeriya.
A yayin wani taron manema labarai a bikin makon likitoci, shugaban kungiyar, Dokts Hassan Salihu, ya jaddada muhimmancin tattaunawa game da barkewar cututtuka tare da daukar matakan kariya.
- Muna Fama Da Taɓarɓarewar Tattalin Arziƙi Da Wutar Lantarki – Gwamnonin Arewa Da Sarakuna
- Abubuwan Da Ka Tattaunawa A Taron Gwamnoni da Sarakunan Arewa
Ya bayyana cewa, ko da yake ba a samu rahoton bullar kyandar biri a Kaduna ba zuwa yanzu.
Dokts Salihu ya bayyana matakan da jama’a za su bi don kare kansu, kamar tsaftar jiki, cin abinci mai gina jiki, da kuma kaucewa nau’in wasu dabbobi.
Kungiyar na aiki don dakile yaduwar cututtuka don tabbatar da lafiyar al’umma a jihar.
Sun kuma shirya gangamin wayar da kan jama’a, yin allurar rigakafi, da inganta cibiyoyin kiwon lafiya.
Dokta Salihu ya bayyana mawuyacin halin da likitoci ke ciki a Kaduna, inda ya ce rashin ingantaccen albashi, rashin kayan aiki, da matsalolin tsaro, musamman a yankunan karkara, suna sa likitoci na barin Nijeriya.
A cewarsa wannan matsala ta shafi kiwon lafiya yayin da ma’aikatan lafiya ke neman guraben aiki a kasashen waje.
Kungiyar ta yi kira da a tabbatar da an daidaita albashinsu a fadin Nijeriya domin taimakawa wajen ci gaba da rike kwararrun ma’aikatan lafiya da rage gibin kiwon lafiya.
Dokts Salihu ya bayar da shawarar kafa dokar kasa don sanya mafi karancin albashi ga ma’aikatan lafiya a duk jihohi don a ci gaba da rike kwararru ma’aikatan fannin.
Har wa yau, ya bayyana damuwarsa kan lalacewar wutar lantarki a Arewacin Nijeriya, wanda ke barazana ga rayuwar marasa lafiya.
Kazalika, ya yi kira ga gwamnati ta yi kokari wajen ganin an sako likitar da aka sace, Dokta Ganiyat Popoola.
Likitar ta shafe wata 10 a hannun maharan da suka sace ta.