Allah ya yi wa babban limamin masallacin Juma’a da ke kan titin Maiduguri a Jihar Kaduna, Sheikh Dahiru Lawal Abubakar, rasuwa.
Sheikh Dahiru, ya rasu da safiyar yau Laraba, za a yi Jana’izarsa da misalin karfe 1:00 na rana yau Laraba a masallacin da yake limanci da ke kan titin Maiduguri a Jihar Kaduna.
Muna Addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kyauta karshenmu, idan tamu ta zo yasa mu cika da imani, Amin.