• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Lokaci Ya Yi Da Za A Mayar Da Kayayyakin Tagulla Na Daular Benin Gida

by CGTN Hausa
2 years ago
Benin

Gidan adana kayayyakin tarihi na Burtaniya, wato the British Museum a Turance, ya kasance daya daga cikin gidajen adana kayayyakin tarihi mafi girma kuma mafi dadadden tarihi a duniya, sai dai da yawa daga cikin kayayyaki sama da miliyan 8 da ke gidan, an kwato ko sato su ne daga kasa da kasa a lokacin da Birtaniya ke mulkin mallaka a sassan duniya. 

Misali a gidan, akwai kayayyakin tagulla kimanin 900 na daular gargajiya ta Benin wadda a zamanin da ta kasance a kudancin kasar Nijeriya, wadanda Burtaniya ta kwaso su gidan bayan da ta wawushe fadar daular a lokacin da ta kaddamar da yaki kan daular a shekarar 1897. Wadannan kayayyakin tagulla dai sun kasance masu matukar muhimmanci a tarihin fasahar Afirka, haka kuma kayayyakin tarihi masu daraja na al’ummar Nijeriya. Ban da su, a gidan, akwai sassakan marmara na Parthenon na kasar Girika, da dutsen Rosetta na kasar Masar da ma wasu kayayyakin tarihi masu daraja dubu 23 da suka fito daga kasar Sin, wadanda suka shaida mummunan tarihin mulkin mallaka na Burtaniya.

  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Kaucewa Aiwatar Da Matakan Da Ka Iya Barazana Ga Tsaronta
  • Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Ga Amurka Game Da Batun Sayarwa Taiwan Makamai

Duk da cewa kasashen Sin da Nijeriya da Girika sun sha bukatar Burtaniya da ta mayar musu da wadannan kayayyakin tarihi, amma kullum Burtaniya ta kan ki bisa dalili na wai “kare lafiyar kayayyakin”. Amma abin kunya shi ne, a cikin kusan shekaru 30 da suka gabata, gidan adana kayayyakin tarihi na Burtaniya wanda ke daukar kanta a matsayin mai kare lafiyar kayayyakin tarihi, ya sha fuskantar sace-sace a kalla sau shida. Wani rahoton bincike na baya-bayan da gidan ya fitar, ya kuma nuna cewa, daga cikin kayayyakin da gidan bai nuna su ba, akwai kimanin 2000 da suka bace ko aka sace su ko kuma suka lalace.

A game da yanayin tsaro na kayayyakin tarihi da ke gidan, Abba Isa Tijani, babban darektan kwamitin kula da gidajen adana kayayyakin tarihi da kayayyakin tarihi na Nijeriya ya ce, “wasu kasashe da gidajen adana kayayyakin tarihi sun sha bayyana mana cewa, kayayyakin tagulla na daular Benin ba su da tsaro a Nijeriya, amma ga yadda aka sace su. Ainihin batun shi ne kayayyakin tarihi ne da aka kwashe, kuma ya kamata a mayar da su gidanjensu ko kasashensu na asali.”

Zamanin mulkin mallaka ya shude, kuma shekaru sama da 120 ke nan da aka kwace kayayyakin tagulla na daular Benin daga Nijeriya, lokaci ya yi da za a mayar da su gida. (Mai Zane: Mustapha Bulama)

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
Kafafen Yaɗa Labarai Ne Manyan Dirkokin Dimokraɗiyyarmu – Minista

Kafafen Yaɗa Labarai Ne Manyan Dirkokin Dimokraɗiyyarmu - Minista

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.