Shugaban Hukumar Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) Isah Jere Idris ya yi kiran samar da haɗin kai a tsakanin hukumomin tattara bayanai a ƙasar nan don cimma nasarar samar da rumbun bayanai na bai-ɗaya na Nijeriya domin haɓaka ci gaban ƙasa.
Ya yi wannan kiran ne a hedikwatar hukumar ta shige da fice yayin da yake karɓar baƙoncin tawagar gudanarwa na Shirin Bunƙasa Samar Da Bayanan Shaida Domin Ci Gaba (DID4D) a ziyarar ban girma da suka kai masa.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in Sadarwa na NIS, ACI Amos Okpu, ta yi bayanin cewa shugaban hukumar, CGI Isah Jere ya jaddada muhimmiyar rawar da tattara bayanai da sarrafa su za su taka a kan sha’anin tsaro da tsare-tsaren ƙasa.
“Muna rayuwa ne a lokacin da bayanai suka zama wata babbar kadara don ƙarfafa ƙasa kuma haƙiƙa sashen bayanan yana gwagwarmayar ƙwace wa arzikin mai kambunsa na kawo arziki a duniya; don haka akwai bukatar mu haɗa kai don inganta bayanan ƙasa. Ba za mu iya ci gaba da yin watsi da bayananmu suna zaune kara-zube a cikin rumbunan adana su ba a tsakanin hukumomi daban-daban. Lokacin daidaita su su zamo bai-ɗaya ya yi”, in ji shi.
Kwanturola Janar ɗin ya ci gaba da cewa, hukumar a matsayinta na mai taka muhimmiyar rawa a tsarin bayanan ƙasa tun daga shekarar 2019 ta nuna ƙwarin gwiwa wajen cimma daidaiton tsarin bayanan ‘yan ƙasa tare da ɓullo da ingantaccen fasfo na zamani (ePassport) wanda ya wajabta bayar da lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) ga duk mai neman fasfon.
Ya kuma lura cewa hukumar ta NIS tana ci gaba da zuba jari a tsarin tattara bayanai da sarrafa bayanan ta na’urorin da take aiki da su a sassa daban-daban da suka haɗa da Kan Iyakoki don tabbatar da ingantaccen tsarin bayanai. Ya ba da tabbacin cewa NIS za ta ci gaba da kasancewa a shirye a koyaushe don yin haɗin gwiwa tare da hukumomin da abin ya shafa don cimma cikakkiyar daidaituwar bayanan shaida na ƙasa don gudanar da kyawawan tsare-tsare da ci gaban ƙasa.
Tun da farko, Babban Jami’in Gudanarwa na DID4D, Mista Solomon Musa Odole ya sanar da cewa tawagarsa ta ziyarci hedkwatar NIS ce don neman haɗin gwiwa kan aikin tantance bayanan shaida a zamanance.
Ya bayyana ƙudirin tawagarsa ta tattaunawa mai ma’ana tare da haɗin gwiwa da NIS don cimma burin Gwamnatin Tarayya na haɓakawa da ƙarfafa tsarin da ake amfani da shi na tattara bayanan shaida da nufin ƙara yawan mutanen da ke da takardar shaidar ƙasa.
A cewarsa, yin hakan zai ƙara sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa damar samun muhimman ayyuka, da inganta hanyoyin samar da ayyuka da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya ta fuskar zamani.
Ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da ƙoƙari sosai ciki har da tattaunawa kan manufofin ƙasa da masu ruwa da tsaki wajen samar da dokar kare bayanan sirri ta ƙasa ko sake duba dokokin da ake da su domin tabbatar da cewa an samar da tsare-tsare na hukumomi da suka dace don ciyar da tattalin arzikin ƙasa gaba.
Shirin DID4D dai wani shiri ne na Nijeriya, wanda Bankin Duniya, da Bankin Zuba Jari na Turai da Hukumar Raya Faransa suka ɗauki nauyin gudanar da shi da nufin ƙara yawan mutanen da ke da Lambar Shaida ta ƙasa (NIN) da aka samar ta sahihiyar hanya mai ƙarfi.
Babban jami’in shirin ya samu rakiyar sauran ma’aikatan shirin da suka haɗa da Dakta Walter Duru, Manajan Sadarwa na cikin gida, Bamidele Akinola, Akantan Shirin da Mouktar Adamu, Manajan Sadarwa da dai sauransu.
NIS dai ta duƙufa ka’in da na’in wajen tabbatar da bayanan duk wasu harkoki na shige da fice da suka shafi baƙi da ‘yan ƙasa. Inda ta samar da na’urorin tattara bayanan da tantance su a filayen jiragen sama da iyakokin ruwa da na kan-tudu.