Wani matashi mai aikin sharar jirgin sama na Kamfanin Kula da Harkokin Jiragen Sama na Nijeriya (NAHCO), Auwal Ahmed Dankode, ya nuna gaskiya, yayin da ya tsinci dala $10,000 a cikin jirgi, wanda kuma nan take ya sanar da mahukuntan jirgin game da kudin.
Dankode, wanda ya fito daga kauyen Kode a karamar hukumar Bunkure a Jihar Kano, ya tsinci kudin ne yayin da yake sharar jirgin EgyptAir a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano.
- ‘Yansanda Sun Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Sojoji Suka Yi Wa DPO Wasagu A Kebbi
- Gwamnan Kebbi Ya Yi Alkawarin Sake Gina Gadoji Da Hanyoyin Da Suka Lallace A Jihar
Jirgin ya sauka da misalin karfe 1:30 na rana, a ranar Laraba lokacin da Dankode ya tsinci kudin, wanda ya kai kusan Naira miliyan 16.
Ba tare da bata lokaci ba, Dankode ya sanar da manajan jirgin game da kudin.
Ba jimawaz wani Balarabe ya dawo yana neman kudinsa da suka bata.
Manajan jirgin ya yi masa tambayoyi domin tabbatar da kudin nasa ne, wanda kuma ya tabbatar cewa kudin nasa ne, sakamakon hujojjin da ya bayar.
Mutumin ya ji dadin samun kudin nasa sosai har ta kai ga ya rungumi Dankode, tare da nuna godiyarsa kan yadda ya nuna gaskiya.
Yayin da yake magana kan lamarin, Dankode ya ce, “Mutane da yawa a filin jirgin sun daga ni sama suna yaba min bisa abin da nayi. Na ji dadi sosai kuma ina farin ciki. Ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar farantawa wani.
“Ina yin aikina ne lokacin da na tsinci kudin. Na san nan take cewa ya kamata na sanar. Wannan ne abin da ya dace a yi,” in ji shi.