Akanta da jami’in kula da dakin ajiye kayayyaki na ma’aikatar gona da albarkatun kasa na jihar Nasarawa sun shiga hannun da zarginsu da ake yi na karkatar da tiraktocin guda tara na Takin zamani da aka samar da zimmar raba wa manoma a sassan kananan hukumomin 13 da ke jihar.
Kwamishinan ma’aikatar gona ta jihar Hon. Nuhu Ibrahim-Oshafu, shine ya shaida hakan a lokacin da jami’an ma’aikatar gona na jihar Nasarawa da ma’aikatar bunkasa harkokin gona ta jihar (NADP) suka bayyana a gaban kwamiti domin kare kwazon kasafin kudi na 2022.
- Wang Yi Ya Yi Tsokaci Kan Matsayar Sin A Batun Tekun Kudancin Kasar
- Ko Kananan Sana’o’i Na Biya Wa ‘Yan Nijeriya Bukatunsu?
Ibrahim-Oshafu, ya ce, ma’aikatar ta sayo da raba tiraktoci Taki 21 da aka sayo a kan kudi naira miliyan N238 a jihar.
Ya ce a lokacin da ya shiga Ofis domin kama aiki, 12 da rabin tiraktocin takin ne aka mika masa, ya ce amma da suka je dakin ajiye kayayyaki sai suka gano tiraktocin 9 sun yi baton dabo.
Ya ce an cafke Akanta da jami’in kula da dakin ajiye kayayyaki bisa zargi da hannu a bacewar takin kuma tunin aka dakatar da su a yayin da bincike ke cigaba da gudana kan lamarin.
Shi kuma Manajan NADP, Mr Emmanuel Allahnana, da ya bayyana a gaban kwamitin ya ce akwai karancin malaman gona da jihar ke fama da shi don haka ya roki a dauki karin ma’aikata domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a fannin harkokin noma domin bunkasa harkokin abinci a jihar.
Da yake maida bayani kan batutuwan da suke akwai, Shugaban kwamitin gona na Majalisar Dokokin Jihar, Mr. Ibrahim Peter-Akwe, ya roki gwamnatin jihar ta ayyana dokar ta baci a bangaren noma, ya kuma gargadi ma’aikatan dangane da karancin Taki da manoma ke samu a jihar.
Ya ce fannin gona na da muhimmanci a jihar don haka da bukatar gwamnati ta dauki matakan shawo kan matsalolin da suke akwai a bangaren gona.