Shugabancin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) sun dakatar da yajin aikin da kungiyar ta fara, na tsawon makonni biyu.
Matakin dai ya biyo bayan zaman sulhun da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da ma’aikatan wutar lantarkin da ke yajin aikin, wanda aka gudanar da zaman a Abuja ranar Laraba.
- Ma’aikatar Sarrafa Kwakwa A Nijeriya Na Bukatar Wutar Lantarki -Dapo
- Jami’an Tsaro Sun Cafke Barayin Wayar Wutar Lantarki A Kano
A karshen taron wanda ya dauki tsawon sa’o’i uku ana yi, ma’aikatan sun amince da dakatar da yajin aikin, lamarin ya jefa masana’antu kasar cikin duhu.
Ma’aikatan sun bayyana fatansu na cewa gwamnati za ta mayar da hankali tare da tabbatar da walwalarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp