Ana iya fuskantar babbar matsala a samar da wutar lantarki a kasa yayin da Kungiyar Kwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) ta yi barazanar rufe ayyukan samar da wuta a fadin kasa, bayan wani zargin harin da jami’an ‘yansanda masu makamai suka kai wa ma’aikatan Kamfanin Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) a Egbu 132/33kB Transmission Substation da ke Jihar Imo.
Kungiyar ta fada a matsayin martani ga abin da ta kira “shigar da makami cikin tashin hankali”, ta riga ta umurci membobinta da su dakatar da ayyukan samar da wuta a Jihar Imo har sai an ba da sanarwar gaba.
- Ko Sabon Shugaban PDP Zai Iya Magance Matsalolin Jam’iyyar Kuwa?
- Gwamnan Kano Ya Ɗauki Malaman Lissafi 400 Aiki
NUEE ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan da ma’aikatan da ke aiki aka ce an doke su da makamai, wasu kuma aka sace su ta hannun jami’an ‘yan sanda da ake cewa suna aiki bisa umarnin gwamnatin jihar.
Wannan yananyi ya jawo fushi sosai a cikin sashen samar da wuta, inda kungiyar ta yi gargadi cewa za ta dakatar da ayyuka a fadin kasa sai dai idan hukumomi sun dauki mataki nan take don tabbatar da tsaro da kariya ga ma’aikatan wutar lantarki a duk fadin Nijeriya.
An ce ‘yansanda, wadanda ake cewa suna aiki ne a madadin gwamnatin jihar, sun shiga dakunan sarrafa wutar na tashar Egbu 132/33kB Transmission Substation da karfi, inda suka lalata kayan aiki kuma suka hana gudanar da ayyuka.
Ana zargin an afka wa ma’aikatan da makami, an doke su, yayin da aka sace wasu zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
A cikin wata sanarwa daga Sakataren Gudanarwa na Kungiyar NUEE, Dominic Igwebike, a daren Asabar, an ce: “NUEE na nuna matukar mamaki da fushi kan irin halin ‘yan ta’adda da rashin kwarewa da jami’an ‘yansanda suka nuna a yayin da suke aiki a madadin gwamnatin Jihar Imo.
“Wadannan jami’an sun kutsa da karfi cikin dakunan sarrafa wuta a Egbu 132/33KB Transmission Substation domin tilasta wa masu aiki su bayar da dakatarwar wuta ta haramtacciya.
“Yayin harin, ana zargin jami’an sun katse wuta da karfi, sun rike dukkan ma’aikatan da ke aiki a matsayin garkuwa, suna tilasta musu bude breakers cikin matsin lamba.
“Bugu da kari, sun yi amfani da tashin hankali kan membobinmu, suna duka, cin zarafi da duk wani ma’aikaci da suka gani. An lalata kayan kansu, ciki har da wayoyi, kwamfutoci, da motoci, haka kuma an lalata na’urorin CCTB.”
“Jami’an ‘yansanda sun aiwatar da wannan mummunan harin bakin ciki da rashin imani ga ma’aikata marasa laifi kuma sun sace su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
“NUEE na bayyana kiyayya sosai ga wannan abin kunya kuma tana bukatar a sako mambobinmu da aka sace nan da nan. Haka kuma, muna kiran TCN, Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya, da Babban Jami’in ‘Yansanda (IGP) da su bayar da tabbacin kare membobinmu da hana faruwar irin wannan tashin hankali daga ‘yan sanda ta hanyar sanya su a kulawa.
“Bugu da kari, muna bukatar a maye gurbin duk wani kayan ma’aikata da aka lalata ko aka kwace, sannan muna tabbatar da cewa duk ma’aikatan da aka duka su samu cikakken kulawar lafiya.
“Saboda haka, NUEE ta umurci dukkan membobi su nisanci ofis har sai an ba da sanarwa ta gaba, domin ba za mu iya ci gaba da aiki a yanayin tashin hankali, tsangwama, da barazana ga rayuwa ba. Za a iya ci gaba da aiki ne kawai idan an tabbatar da tsaron ma’aikata da kayan aiki gaba daya.
“Idan ba a magance wadannan matsaloli cikin gaggawa ba, kungiyar ba za ta samu wata hanya ba face ta dakatar da ayyukanmu a fadin kasa har sai an tabbatar da isasshen tsaro da kariya a duk wuraren aiki.”














