• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Haifar Da Sabon Salo Na Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Haifar Da Sabon Salo Na Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta zarce tsohon tunanin kasa da kasa, na neman moriya bisa bambancin labarin kasa, tare da samar da wani sabon salo na hadin gwiwar kasa da kasa.

Wang ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata.
An ce, nan da shekaru tara bayan gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, ta haifar da babban tasiri a duniya.

  • Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Za Ta Karfafa Alakar Tattalin Arzikin Afirka Da Sin

A sa’i daya kuma, ana tsokaci da cewa, kasar Sin na inganta shawarar domin cimma moriyarta a fannin siyasa. Game da wannan batun, Wang ya jaddada cewa, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya ” ba rufaffiyar da’ira ba ce, maimakon haka babban dandamali ne budadde kuma mai hade da bangarori daban daban.

Kana shawarar ba kasar Sin ce ke “yin kidanta ta yi rawar ta ita kadai ba”, maimakon haka “rawa ce da take takawa” tare da sauran abokai.

A cewarsa, kasar Sin a bude take ga duk bangarorin da suka shiga ayyukan raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, kuma a shirye take don yin la’akari, da hade shawarar raya manyan ababen more rayuwa da wasu kasashe suka gabatar, don samar da duniya da kayan aikin jama’a masu inganci.

Labarai Masu Nasaba

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

Yayin da yake ba da amsa kan muhimmancin ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam kan duniyar dake halin yanzu, Wang ya bayyana cewa, a duniyar yau dake fama da yaduwar annobar COVID-19, tabarbarewar tattalin arziki, da rikice-rikice da yake-yake, ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, amsa ce mai karfi ga raba gari ta fannin tattalin arziki, da kafa “kananan kungiyoyi” bisa bambancin ra’ayi da dai sauransu.

Yana da matukar muhimmanci, kuma ya zama tuta mai haskakawa dake jagorantar zamanin yau. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya, Sun Sace Wasu 8 

Next Post

Masu Kwangilar Na’urar Kariyar Korona  Sun Yi Zanga-zanga Kan Rashin Biyansu Kudinsu A Abuja

Related

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya
Daga Birnin Sin

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

14 hours ago
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

16 hours ago
Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

17 hours ago
Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar
Daga Birnin Sin

Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

18 hours ago
Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya
Daga Birnin Sin

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

1 day ago
Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya
Daga Birnin Sin

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

1 day ago
Next Post
Masu Kwangilar Na’urar Kariyar Korona  Sun Yi Zanga-zanga Kan Rashin Biyansu Kudinsu A Abuja

Masu Kwangilar Na'urar Kariyar Korona  Sun Yi Zanga-zanga Kan Rashin Biyansu Kudinsu A Abuja

LABARAI MASU NASABA

APC Na Ƙoƙarin Tarwatsa Mu Ne Saboda Kar Mu Ƙwaci Mulki A 2027 – ADC

APC Na Ƙoƙarin Tarwatsa Mu Ne Saboda Kar Mu Ƙwaci Mulki A 2027 – ADC

September 14, 2025
An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

September 14, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

Rushewar Masa’antu Ya Jefa Al’umma Da Dama Cikin Ƙangin Talauci A Arewacin Nijeriya

September 14, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

September 13, 2025
Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

September 13, 2025
Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

September 13, 2025
An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

September 13, 2025
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

September 13, 2025
An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

September 13, 2025
Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

September 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.