Wasu fusatattun ‘yan kwangilar injinan yaki da cutar Korona da na’urar kariya ta (PPE) ga hukumar birnin tarayya (FCTA) suka gudanar da zanga-zanga a mashigar sakatariyar FCTA, inda suka bukaci a cika musu sauran kudaden kwangilarsu da suke bin hukumar.
‘Yan kwangilar sun nuna damuwarsu kan rashin biyan su kudaden kusan shekara uku, suna masu cewa yanzu ya dace hukumomin da abun ya shafa su biya su hakkinsu.
- Dabarar Da Kasar Sin Ta Dauka Wajen Zamanintar Da Al’umma
- Gwamnati Ta Kama Mutum 80 Da Zargin Taimakawa ‘Yan Bindiga A Jihar Zamfara
Inda suke dauke da alluna masu bayyana sakonsu kai tsaye kamar su “Ya mai girma Minista, ka kawo karshen wannan gazawar, a biya ‘yan kwangilar Korona kudadensu, kudadensu sun kusan kai wa shekara uku.
“Mun gaji da alkawuran karya da ake ta mana,” sannan “Muna bukatar kudadenmu yanzu,” da sauran sakonannin da suke dauke da su.
Tun wajajen karfe 8 na safiya, ‘yan kwangilar suka mamaye yankin Area 11 inda ofisoshin Ministocin Birnin Tarayya da manyan Sakatarori ya ke, inda suka rufe mashigar sakatariyar tare da bayyana damuwarsu da korafinsu.