Wasu rahotanni na cewa, kasar Amurka ta hana masana’antun samar da kananan na’urorin lantarki na kasar Koriya ta Kudu, su cike kason Amurka a kasuwar kasar Sin.
Game da hakan, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting, ta bayyana a gun taron manema labarai da aka kira jiya Alhamis 27 ga wata, cewar hakan ya nuna yadda Amurka, wadda ke sahun gaba ta fuskar kimiyya da fasaha, ke haifar da babban cikas ga cudanyar cinikayya a tsakanin masana’antu yadda ya kamata, tare da karya ka’idojin kasuwanci, da odar cinikayya tsakanin kasa da kasa, yayin da take haifar da barazana ga tsarin samar da kaya na duniya. Don haka kasar Sin ta yi Allah wadai da lamarin da babbar murya.
Shu ta kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga gwamnatin kasar, da masana’antun da abun ya shafa, da su yi la’akarin da moriyarsu cikin dogon lokaci, su martaba ka’idojin cinikayya maras shinge tare da kasar Sin baki daya, a kokarin kafa tsarin samar da kaya mai tsaro da inganci, wanda ke bude kofa ga juna, tare da samun karbuwa daga kowa da kowa a duk fadin duniya, ta yadda za a ci moriya da samu nasara tare.
Game da labarin da wasu kafofin watsa labarai suka bayar cewar, Amurka na kayyade damar zubo wa kasar Sin jari kuwa, Madam Shu ta ce yadda hukumomin gwamnati ke tsoma baki a harkokin kamfanoni bai dace da ka’idojin kasuwanci ba.
Shu ta kara da cewa, nuna bambanci ga wata kasa, da ma kayyade harkokin kasuwanci da ke da nasaba da kasar, ya sabawa babbar manufar ciniki a tsakanin kasa da kasa. Kuma idan labarin ya tabbata, kasar Sin za ta nuna rashin yardarta da hakan da kakkausan harshe. (Kande Gao)