• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ta Maida Martani Game Da Munanan Kalaman Sakataren Tsaron Amurka Kan Kasar Sin

by Sulaiman
3 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ta Maida Martani Game Da Munanan Kalaman Sakataren Tsaron Amurka Kan Kasar Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang, ya amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, dangane da munanan kalaman da sakataren tsaron Amurka ya yi a yayin dandalin tattaunawa na Shangri-La karo na 22, inda ya ce, kalaman sakataren tsaron Amurka din cike suke da ra’ayin nuna babakere da fin karfi, gami da ra’ayin cacar baka, al’amarin da ya kawo babbar illa ga ikon mulkin kan kasar Sin, da jirkita manufofin kasar, don haka kasar ta Sin ta nuna matukar rashin jin dadi da adawa da hakan.

Zhang Xiaogang ya jaddada cewa, batun Taiwan, harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kuma Amurka ba ta cancanci ta nuna yatsa ba, kana bai kamata Amurka ta yi tsammanin yin amfani da wannan batu, wajen taka birki ga ci gaban kasar Sin ba. Tekun kudancin kasar Sin, daya ne daga cikin hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa mafiya hada-hada, kuma mafi tsaro a duniya. Kuma Amurka ce barazana mafi girma ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, ganin yadda take yunkurin gurgunta harkokin tekun kundancin kasar Sin, da hada baki tare da rura wutar rikici tare da wasu sassa.

Jami’in ya kara da cewa, sojojin kasar Sin za su yi kokari tare da kasashen yankin, wajen nuna adawa da ra’ayin babakere dake illata harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik da shigar da rikice-rikice cikin yankin, da kuma kin yarda da duk wani yunkuri na tayar da yake-yake ko zaune-tsaye a yankin. (Murtala Zhang)

Labarai Masu Nasaba

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Tsohon Minista Ya Fice Daga Jam’iyyar APC A Nasarawa

Next Post

2027: Ƙungiyar Shekarau Ta Gindaya Sharaɗi Kafin Shiga Haɗakar Jam’iyyu

Related

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

7 hours ago
Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14
Daga Birnin Sin

Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

8 hours ago
Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12
Daga Birnin Sin

Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

9 hours ago
Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana
Daga Birnin Sin

Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana

10 hours ago
Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025

11 hours ago
Manyan Jami’an JKS Sun Ziyarci Jami’ai Da Mazauna Birnin Lhasa
Daga Birnin Sin

Manyan Jami’an JKS Sun Ziyarci Jami’ai Da Mazauna Birnin Lhasa

12 hours ago
Next Post
2027: Ƙungiyar Shekarau Ta Gindaya Sharaɗi Kafin Shiga Haɗakar Jam’iyyu

2027: Ƙungiyar Shekarau Ta Gindaya Sharaɗi Kafin Shiga Haɗakar Jam’iyyu

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

August 22, 2025
UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

August 22, 2025
Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

August 22, 2025
Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi

Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi

August 22, 2025
JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa

JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa

August 22, 2025
Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

August 22, 2025
Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba

Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba

August 22, 2025
Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana

Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana

August 22, 2025
Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025

Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025

August 22, 2025
Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City

Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City

August 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.