Fitacciyar Jarumar da ke taka rawa a yanzu cikin shiri me dogon zango na Kwana Casa’in da Dadin Kowa, Jarumar da ta ga jiya ta gayau cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, JAMILA SALEH wadda aka fi sani da JAMCY, ta bayyana wa masu karatu bambance-bambancen da ke tsakanin fina-finan baya shekaru goma da suka wuce da kuma fina-finan yanzu.
Kana jarumar ta yi karin haske game da irin mummunan kallon da jama’a ke yi wa matan kannywood, har ma da wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi masana’antar Kannywood din. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
- Abin Da Ya Sa Manoman Katsina Suka Mayar Da Martani Kan Alkwarin Gwamna Radda
- Dalilin Da Ya Sa Kungiyar Sarrafa Taki Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Bincike A Masana’antar
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki…
Sunana Jamila Saleh Muhammad wasu na kira na da Jamcy ko S.Muhammad. An haife ni a Unguwar Tudun Wada ‘Nassarawa Local Gobernment’, Nayi makarantar firamare a ‘Tudun Wada Special Primary School’, Daga nan na tafi ‘Dangana Senior Secondary School’, Sai nayi Sa’adatu Rimi Collage of Education’ nayi NCE, Than na koma na yi ‘BA ed english’ a BUk, yanzu ni ‘class room teacher’ ce.
Ya batun aure da iyalai?
Na yi aure a shekarar 2002 ina da yara biyu, kafin na gama ‘secondary school’ na yi aure, sai kuma auren ya sami damuwa bayan na haifi yara biyu maza, sai na koma makaranta.
Ya aka yi kika tsinci kanki a cikin masana’antar Kannywood, me ya ja hankalinki?
Na fara harkar fim ne don yana bani sha’awa tun ina karama, wato su Hauwa Ali Dodo da su Fati Muhd suna burge ni, kuma na dan fara ‘scene’ biyu zuwa uku a baya, sai na ga ban sami sana’a ba don ina da yara biyu kuma ina kula da su, sai na hakura na koma makaranta, yanzu kuma na ce bari na gwada sa’a ta.
Daga lokacin da kika fara leka masana’antar zuwa yanzu zai kai kamar shekara nawa kenan?
Zai yi ’10 years’ gaskiya, tun lokacin marigayiya Mama Dumba na nan, sanda aka yi fim din ‘Biki Buduri’.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance a wancen lokacin?
Gaskiya akwai kalubale, don kowa cewa yake zai sa ka a fim amma sai kin je wajensa, kamar wasu mayu haka suke a lokacin.
Ya za ki bambanta yadda yanayin shiga fim yake a lokacin baya da kuma yanzu?
Ada ba a fito da yadda mazan ke wa mata wayau ba kamar yanzu, kuma yaran yanzu kamar sun fi mu wayau, mu tarbiyya muka fi su da girmama na gaba.
A lokutan baya akan yi jita-jitan cewa ba a saka mutum a fim sai an fara saka shi a ‘yan rawa, a hankali sai ya fara fitowa matsayin jarumi, shin ke ma kin fara da hakan ko ya abun ya ke?
Ya dangata da hannun wa mutum ya fada gaskiya, idan ‘Producer’ din ya ga za ta iya ‘delibering’ yadda ya kamata wasu za ki ga an sa su kuma cikin kankanin lokaci sun fara ‘acting’ da ‘scene’ biyu, uku.
Ya batun iyaye fa lokacin da kika fara sanar musu cewa kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Na samu gaskiya don ba a son ransu ba, sai daga baya suka amince min don na musu alkawarin zan rike mutuncina da yardar Allah.
Me za ki ce game da batun da mutane ke cewa idan mace ta shiga harkar fim ba ta komawa gidansu sai dai ta ci gaba da zama tare da ‘yan fim din, mene ne gaskiyar maganar?
Ba gaskiya bane, ai yanzu za ki ga abin ya canja kowa burinta ta yi aure, don gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah. Ita mace tana da ‘limited time’ gaskiya don haka ba kowace take kula ‘Yan fim ba ma, Iya ka ci ta yi aikinta ta koma gida.
Da wanne fim kika fara a wancen lokacin, kuma wacce rawa kika taka cikin fim din?
Wani fim ne wai shi ‘Tsarabarmu’ na marigayi Auwal Judge. Na fito a kawar wadda ta ja fim din na so nayi mata kwacen saurayi. Sai Biki Budiri shi ma nayi ‘scene’ biyu.
Da wadanne jarumai kika fara fitowa a fim a wancen lokacin?
Mun yi da Mansura Isah, amma ba zan iya tuna sunan fim din ba gaskiya don an dade, sai wata Jamila, sai Safiya Kishiya.
Za ki iya tuna yawan adadin fina-finan da kika yi a wancen lokacin kafin na yanzu?
Eh! to ba zai fi 7 ba, don gaskiya na bar su na koma ‘school’.
Bayan da kika samu nasarar shiga cikin masana’antar ya kika ji a lokacin, kuma taya kika fara, kasancewar shi ne farkon farawarki?
Na ji wani iri kuma sai na dake don ina da ‘confidence’ a lokacin, amma ba sauki fa ka ga ‘camera’ a kanka dole za ka ji ‘one kind’.
Ya yanayin wahalar daukar aikin ya ke tsakanin na lokacin baya dana yanzu?
Kamar na yanzu ya fi wahala! Dalili kuwa na da ‘sharp-sharp’ ne, yanzu kuwa sai an saita ‘camera’ an saita ‘lights’ an cire duk wani ‘object’ da zai kawo kalubale daga masu kallo, akan ‘shadow’ sai a fasa sai an canja don ka da a gani.
Ya yanayin karatun ‘script’ din, kamar yadda ake cewa a baya ba a zaman hadda nan take ake yi, wanne karin haske za ki yi wa masu karatu akan hakan?
Ai ada kawai cewa za a yi ki ce kaza da kaza, suna baki hasken. Amma yanzu za ki tafi da ‘scripts’ dinki gida ki karanta ‘dialogue’ ki haddace shi, da kuwa ba a yin hakan. Gaskiya na yanzu ya fi sauki shi ya sa labaran za ki ga ya yi daidai da duk ‘scenes’.
Mu koma kan batun kudin da ake bayarwa a lokacin baya, an ce duk fitowa daya na mutum kudinsa naira dari biyar ne, ya gaskiyar zancen?
A baya ba, ana ba ni 2k (2,000) zuwa 1500 kuma akwai abinci isasshe har da nama.
Ya yanayin yadda tsarin na yanzu yake shin akwai ci gaba ta wannan bangaren ko kuwa an samu gazawar hakan?
Ta wani bangaren ya sauya, don yanzu a ‘season’ ana iya ba wa mutum 100k (100,000) ya danganta da wane ‘role’ yake ‘playing’ , kuma fim din na su waye? Akwai ‘Yan kowa ‘producer’ to su za su ce ba da ‘account number’ ga 1k na mota za ki ji ‘alert’ amma fa ba sa biya.
Akwai bambanci na furodusas kenan, wanda mutum zai iya karbar aikinsa ko ya fasa?
Akwai, don ni na dauki fim sana’a, ‘so I see no reason why’ zan bata ta ba lokaci mai yawa kuma babu ‘benefit’, kuma ai ba za su gaya miki babu kudi ba, sai kin yi ‘inbolbed’ ki gane daga baya.
Ya kike da irin wadannan furodusas din idan sun bukaci ki yi musu aiki?
Gaskiya ba na zuwa, ko na fara idan na ga akwai shubuha zan daina zuwa in yi ‘inconclusibe’.
Bayan da kika dawo harkar fim yanzu, kin samu wani kalubale wajen komawar ko kuwa kai tsaye kika shiga ba tare da wata matsala ba?
Gaskiya na samu, wai ba ajina bane yin fim in ji wasu daga cikin kawaye da abokan karatu.
Ya kika ji a lokacin da hakan ya faru, kin yi kokarin hakura ko kuwa?
Sun so su yi ‘discouraging’ dina, amma sai na ce to don me? Wannan fa rayuwata ce, kuma ni ba yarinya karama ba ce yanzu, sai na ci gaba, har na je na kara yin wani ‘audition’ din da ‘Kwana Casa In’, Kuma na fito a ciki kusan ‘scenes’ 15.
Shirin Kwana Casa’in shi ne fim din da kika fara bayan dawowarki kenan?
‘Nope!’ Dadin kowa na fara yi.
Bayan da shirin ya fara fita me mutane suka runka cewa da ke akai, kamar yanayin yadda kikai aktin din, musamman yadda a baya suka rinka yunkurin hanaki komawa?
Na sha waya, har na ji dadi na gode Allah, “Kin yi kokari, acting naki ya burge mu kamar likitar gaske wallahi”. kawayena ma sun sha kira ana tambaya “wai Jamila na gani a Dadin Kowa ‘as’ Likita?”.
Wace rawa kika taka a cikin shirin kwana casa’in da kuma Dadin kowa?
A dadin kowa likita nake fitowa mai gaskiya da son taimakon mutane ga wasa da dariya, kwana Casa’in kuma a kanwar Hajiya Rabi Bawa Mai Kada, kuma ‘yar gidan Baba Hakimi wato Mal. Rabe.
Bayan Dadin Kowa da Kwana Casa’in da kika yi a dawowarki fim, kin yi wasu fina-finan ne?
Gaskiya ban yi ba, iya su biyun nake don ina da aiki kamar yadda na fada a farko, sannan mun je Daura wani aiki da Dutse amma fa kasawa nayi don na ga Ulcer ta za ta tashi.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta cikin masana’antar?
Ba za a rasa ba, kamar tsangwama daga matan, Kin zo – na zo kawai sai a fara yi miki kallon uku ahu, irin kallon wannan kuma daga ina?
Wanne irin nasarori kika samu game da fim?
Wato ko ‘scene’ daya mutum ya yi idan Allah ya so daga shi zai daukaka, Alhamdu lillah ina ganin mutuntawa da darajawa daga wajen mutane daban-daban, har da yara kanana, a ce mu yi hoto ko ki ga mutum ya haife ka amma yana baka girma da darajawa, ina kara godewa Allah.
Ya kika dauki fim a wajenki?
Sana’a ce wacce zan ci abinci da ita, ko na ce nake cin abinci da ita.
Ya kike iya hada aikinki da sana’ar fim?
Aiki na koyarwa ne, don haka ina da ‘time’ misali idan an tashi ‘school’ zan iya zuwa, Idan ana hutu ina samin isashshen lokaci nayi wasu abubuwan.
Me kike son cimma game da fim?
Ina son na yi fim nawa na kaina kuma in yi suna a duniya.
Da wanne Jarumi ko Jaruma kika fi so a hada ki a fim?
Kowa ma, amma ban da wanda ba ya iya rike ‘lines’ dinsa, suna bani wahala.
Wace ce babbar kawarki a Kannywood?
Gaskiya ba ni da kawa, sai dai muna mutunci da Hajia Maryam CTB.
Kina da ubangida a masana’antar Kannywood?
‘Nope’! ba ni da shi gaskiya, sai dai zan yi ‘soon’.
Wanne waje ne a cikin shirin Dadin kowa ya ba ki wuya, wanne ne kuma ya fi saka ki dariya a duk lokacin da kika tuna?
Wanda ya bani wahala shi ne wajen da wata ‘Nurse’ take wulakanta ‘patients’, na zo na yi mata fada na ce ka da ta kara. An dade ana dauka amma ba a sami abin da ake so ba har na galabaita. Wajen da ya ba ni dariya shi ne inda Malam Na Ta’ala yake suma sanda aka ce cikin Adama ba ciki ba ne karin mahaifa ne.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba?
Lokacin da aka biya min makka wato Umrah, da kuma sanda na gama karatu ba tare da ‘carry ober’ ba.
Yaushe kike sa ran kara yin aure?
Duk lokacin da miji ya fito min zan iya aure ba bata lokaci.
Idan kika yi aure a yanzu shin za ki ci gaba da yin fim ne ko za ki ajjiye?
Idan har mijin ya amince na ci gaba to zan yi, ai ‘Business’ ne.
Me za ki ce ga masoyanki da kuma masu kallon fina-finanki, musamman masu yi wa ‘yan fim mummunan kallo game da rashin yin aure sun tare a harkar fim da sauran zantukan da ke yawo a gari?
Ina so su gane cewa ita mace zuwa ake a ce ana son ta kuma a kawo mata kudin aure, ba kamar namiji ba da zai so ya aure ta a sati biyu. Kuma ita rayuwar kowa a rubuce take tunda ka zo duniya har ka bar ta. Don Allah a dinga yi mana kyakkyawan zato a matsayinmu na musulmai, ‘ya’yan wasu kuma iyayen wasu, sannan matan wasu.
Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga sana’ar fim, har ma da wadanda ke ciki?
Su rike mutuncin kansu, ita mace aba ce mai daraja, ba sai kin ba da kanki za ki yi suna ba, daukaka daga Allah ne don haka mu ji tsoron Allah.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da ci gaban masana’antar Kannywood?
Zan so a dinga basu jari kuma gwamnati ta kirkiro musu ‘seminar’ da ‘workshop’ na yadda za su dinga gyara ayyukan da ya shafi fim, a nuna mahimmanci dan Adam ka da a kira shi aiki idan babu kudi ko abinci sannan a dauki sana’ar da gaske a sa mata ‘capital’.
Me za ki ce da makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Ina yi muku fatan alkhairi ko yaushe, idan mun yi kuskure a dinga gyara mana ban da kalaman batanci, Lobe u all.
Me za ki ce da ita kanta LEADERSHIP Hausa?
Allah ya kara muku daukaka ku je Inda baku tunanin zuwa. Ya karawa ma’aikatanku lafiya da arziki mai dorewa.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Fatan alkhairi ga mahaifiyatah abar alfahari na, sai ‘ya’yana guda biyu Abdullah Sadi Saleh da Ibrahim Sadi Saleh.