ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Da Ya Sa Kungiyar Sarrafa Taki Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Bincike A Masana’antar

by Abubakar Abba
3 years ago
Taki

Babban sakataren kungiyar masu sarrafa Takin zamani da rabar da shi  na kasa FEPSAN Mista  Gideon Nagedu ya bukaci  shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu da ya yi bincike akan masana’antar samar  da Takin zamani kan yadda ta kasance a shekaru bakwai da suka gabata.

Nagedu a wata hirarsa da manema labarai ya bayyana cewa, abinda muka bukata daga gun gwamnatin shugaba Tinibu shine ya yi bincike akan masana’antar samar  da Takin zamani kan yadda ta kasance a shekaru bakwai da suka gabata.

  • Hajjin Bana: NAHCON Ta Samar Da Biza 73,310, Tare Da Kai Alhazai 46,000 Kasar Saudiyya
  • Zan Yi Aiki A Bayyane Tare Da Shugabannin Majalisa Ta 10 – Tinubu

Sai dai, sakataren ya yi nuni da cewa, idan zamu yiwa tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari adalci, gwamnatin ta samar da gagaruwar ci gaba wajen habaka fannin samar da Takin zamani a kasar nan

ADVERTISEMENT

Ya ci daga da cewa, a lokacin tsohuwar gwamnatin ta Buhari, an samar da Takin zamani da ya karu zuwa tan miliyan 1.6 wanda wannan ne ya kasance na karon farko a kasar nan.

“An samar da Takin zamani da ya karu zuwa tan miliyan 1.6 wanda wannan ne ya kasance na karon farko a kasar nan a lokacin tsohuwar gwamnatin Buhari.”

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Nagedu ya kara da cewa, za ka iya gani da Idonka a karkashin shirin samarr da Takin zamani na fadar shugban kasa a lokacin tsohuwar gwamnatin ta Buhari, an samar da ci gaba matuka.

A cewarsa, a kungiyance, duk irin nasarar da tsohuwar gwamnatin ta Buhari ta samar a fannin aikin noma a kasar nan, muna kira ga shugaba Tinibu da ya dora kan sanar da gwamnatin baya ta samar a fannin.

“Duk irin nasarar da tsohuwar gwamnatin ta Buhari ta samar a fannin aikin noma a kasar nan, muna kira ga shugaba Tinibu da ya dora kan sanar da gwamnatin baya ta samar a fannin.”

Daya bangaren da muka bukatar gwamnatin ta Tinubu ta mayar da hankaili akai Sakataren ya sanar da cewa, muna kira ga Tinubu da ya mayar da hankali wajn bunkasa samar da kudaden musaya na ketare, inda hakan zai kara bai wa habaka fannin na aikin noma.

Ya bayyana cewa, daya bangaren da muka bukatar Tinubu ya mayar da hankali akai shine magance yadda wasu masu sarrafa Takin zamani ke gurbata shi, inda hakan ke janyo wa masu zuba jari a fannin da kuma manoma asara.

A cewarsa, matukara gwamnatin ta kawo karshen wannan matsalar, manoman kasar nan za su samu sukunin yin girbe amfanin gonakan su mai yawa.

“Muna bukatar shugaban kasa Tinubu ya mayar da hankali akai shi ne magance yadda wasu masu sarrafa Takin zamani ke gurbata shi, inda hakan ke janyo wa masu zuba jari a fannin da kuma manoma asara.”

A wani labarain kuwa, Manoman Albasa sunce sun yi asarar sama da Naira biliyan uku a duka shekara saboda rashin sarrafa ta yadda ya dace a cikin kasar nan.

Shugaban kungiyar manoman Albasa da sararrafa ta na kasa Isah Aliyu ya bayyana hakan, inda ya ce, Nijeriya  na noma Albasa metric tan miliyan biyu na Albasa a duk shekara.inda hakan ya kai kimanin kashi 40 a cikin dari na jimlar Alabsar da ake nomawa a kasar.

“Nijeriya na noma Albasa metric tan miliyan biyu na Albasa a duk shekara.inda hakan ya kai kimanin kashi 40 a cikin dari na jimlar Alabsar da ake nomawa a kasar. “

Aliyu wanda ya sanar da hakan a taron kaddamar da kamfanin sarrafa Albasa da Tafarnuwa wanda ya kasance irinsa na farko a jihar Sokoto ya ci gaba da cewa, duk da cewa Nijeriya ta kasance kan gaba wajen noman Albasa da Tafarnuwa a duniya, amma ta kasance tana shigo da amfanin cikin kasar nan saboda rashin kayan da za a sarrafa wadannan amfanin biyu.

“Kasance irinsa na farko a jihar Sokoto ya ci gaba da cewa, duk da cewa Nijeriya ta kasance kan gaba wajen noman Albasa da Tafarnuwa a duniya,  amma ta kasance tana shigo da amfanin cikin kasar nan saboda rashin kayan da za a sarrafa wadannan amfanin biyu.”

Shugaban ya kara da cewa, rashin kayan da za sarrafa amfanin biyu a kasar nan, na ci gaba da zamowa manoman da ke noma su, babban tarnaki.

A cewarsa,”Sama da metric tan miliyan biyu 2 na Albasa ake nomawa a kasar nan a duk shekara,  inda jihar Sokoto ke noma kashi 40 a cikin dari.”

Taki
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Abin Da Ya Sa Manoman Katsina Suka Mayar Da Martani Kan Alkwarin Gwamna Radda

Abin Da Ya Sa Manoman Katsina Suka Mayar Da Martani Kan Alkwarin Gwamna Radda

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.