Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta bai wa waɗanda suka yi nasara a zaɓen ƙananan hukumomi takardar shaidar lashe zaɓe.
Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Malumfashi, ne ya gabatar da takardun ga sabbin shugabannin ƙananan hukumomi guda 44.
Daga cikin sabbin shugabannin akwai Sa’adatu Yushau Tudunwada, wata matashiya da aka zaɓa a matsayin shugabar ƙaramar hukumar Tudunwada.
A jawabin da ta gabatar, Sa’datu ta yi alƙawarin tabbatar da adalci ga kowa a yankin da take shugabanta, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.