Abin takaici ne a halin yanzu lamarin rashin aikin yi a tsakanin matasanmu yana ta karuwa duk kuwa da dinbin arzkin albarkatun kasa dana mutane da Allah ya hore mana.
Lamarin a duk shekara sai kara karuwa yake yi inda matasa da suka kammala karatunsu na jami’a da sauran manyan makarantu ke cika kasuwar neman aiki da fatan samarwa kansu hanyar neman rufawa kansu asiri, sai kawai su fahimci babu wata fata a garesu na samun aiki a duk inda suka fuskanta, a haka kuma zaka ga matasa da yawa suna yawo a kan titunan mu suna talla, adaidai lokacin da ya kamata a ce suna can sun samu aiki mai muhimmanci da za su fuskanci rayuwar da ta kamata. A rahoton wata cibiya mai zaman kanta mai suna JPMG yawan matasa marasa aiki a Nijeriya ya kai kashi 37.7 a shekarar 2022.
Hasashe ya kuma nuna cewa, yawan marasa aiki zai ci gaba da karuwa zuwa kashi 40.6 a shekarar musammna ganin yadda masu neman aikin ke kara karuwa a sassan Nijeriya.
Cibiyar ta nuna tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin kasa ke yi da kuma ganin ba yadda zai iya karbar sabbin matasa fiye da miliyan 4 zuwa 5 da suke shigowa fagen fafutukar neman aiki a duk shekara. A bin talkaici a nan shi ne a halin yanzu Nijeriya ce a kan gaba a fadin duniya na kasar da ta fi kowace kasa yawan marasa aikin yi, kamar dai yadda kiddigar da aka fito da ita a kwanan nan ta nuna.
Yawan marasa aiki a Nijeriya ya kai fiye da kashi 33.3, wannan abin tsoro ne don kuwa mun zarce yawan na kasar Afirka ta Kudu da suke da kashi 32.9 da kasar Iran mai kashi 15.55. Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS bata kai ga fitar da rahoto na wannan shekarar ba zuwa yanzu, Babu wanda zai iya karyata wannan lamarin. Rashin aiwatar da tsare-tsaren da za su kai ga bunkasa tattalin arzikin kasa ya ci gaba da zaftare abin da yake shiga aljihun al’ummar kasa gaba daya. Yadda al’ummar Nijeriya ke karuwa da kashi 3.2 yana kara tabarbare lamarin rashin aiki ga matasa. Barnar lamarin rashin aikin yi a cikin al’umma ya tashi daga na tattalin arziki zuwa haifar da kanana da manyan laifukka a tsakanin matasa a sassan Nijeriya.
Masana sun danganta karuwa rashin aikin yi a tsakanin matasa da yadda ake samun karuwar matsalar tsaro da aikata muggan aiki. Rashin aiki yana tunzura mutane fadawa ayyukan rashin gaskiya saboda neman hanyoyin neman mafita na rayuwa, wanda hakan kuma ke haifar da karywar matsalolin tsaro a sassan Nijeriya. Wani abin tayar da hankali kuma shi ne yadda matsalolin tsaro kamar fashi da makami, kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci suka ci gaba da karuwa sadoda yadda masata ke fuskantar rashin aikin yi kuma gashi suna so rafa wa kansu asiri.
Tsaface-tsaface, da yadda ake karrama wadanda suka yi kudi ta hanyar da bata dace ba, a bayyana yake a halin yanzu kungiyoyin masu aikata laifukka suna ta kara karfi a sassan Nijeriya. Jami’an tsaro na ta fafutukar ganin sun kawo karshen masu aikata laifi ba tare da samun nasarar da ake bukata ba, haka ya kai wasu gwamnoni sun yi watsi da hakkin da yake kansu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma sun bar al’umma a hannun ‘yan ta’adda suna cin karensu babu babbaka. Ayyukan ta’addanci da dama da suka hada da garkuwa da mutane da zaluntar marasa karfi yana ta daukar sabon salo a cikin al’umma. Wadannan ayyyukan ta’addanci yana kara karfafa karin maganan nan ne da ke cewa, zuciyar da ba a bata aiki ba za ta nema wa kanta aiki.”
Ra’ayin wannan jaridar a nan shi ne, wadannan matsalolin sun taimaka matuka wajen durkushe ci gaban kasar nan. Binciken da aka gudanar daban-daban musamman ma wanda Ezeajughu Mary C. (PhD), ya yi, ya nuna danganta ta kut da kut a tsakanin rashin aikin yi da yadda ayyyukan ta’addanci suke habbakar a Nijeriya.
Babu shakka a kwai hanyoyin magance matsalaer rashin aikin yi a tsakanin matasa, wanda baya ga magance matsalolin tsaro zai kuma tabbatar da bunkasar tattalin arzikin kasa ba tare da bata lokaci ba. A kan haka ya kamata dukkan gwamnatoci a dukkan mataki su karfafa kokarin su na samarwa matasa ayyukan yi a duk inda suke a fadin kasar nan.
Ganin muhimman kanana da matsaikar masanan’antu da kuma yadda manyan kamfanoni ke gudu zuwa kasashen su, ya kamata a rungumi farfado da sabbin kananan masa’anantu ta haka za a tabbatar da bunkasar tattalin arzikin kasa.
Dole gwamnati ta samar da yanayi mai muhimmanci da zai kai ga bunkasa rayuwar matasa tare da samar musu da ayyukan yi, wannan na daga cikin abubuwan da za su kawar da hankalinsu daga aikata laifukka, a kan haka a kwai bukatar samar da dokokin da za su rage wahalhalun da ake fuskanta wajen kafa kamfanoni da cire harajin da ake karba a wajen masu niyyar kafa masana’antun a fadin Nijeriya.