Wani magidanci mai shekaru 45, Yusuf Muhammad, a ranar Litinin, ya roki wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna, da ta umurci matarsa, Murjanatu Nasiru, ta biya shi Naira miliyan 1,600,000 domin a raba aurensu.
Muhammad ya roki kotun ne sabida matarsa Murjanatu ta nemi ya sake ta, ta hanyar fansa (Khul’I). Inji Daily trust
A baya dai, Murjanatu ta yi alkawarin maidowa Muhammad Naira N30,000 da ya biya a matsayin sadakinta.
“Na ba ta Naira 50,000 a matsayin sadaki, ba Naira 30,000 ba, kuma ta sa na rasa naira N35,000 na wata-wata da nake samu daga ‘yan uwana.
“Tun da muka yi aure a shekarar 2018, ’yan’uwana sun daina aiko mini da alawus din wata-wata saboda na aure ta.
“Saboda haka, sai ta biya ni kudin kafin ta raba aurenta da ni,” in ji Muhammad.
Murjanatu, ta bakin lauyanta, Abubakar Abdullahi, ya ce babu wata yarjejeniya da ta rigaya ta biyan wadannan Kudaden akan wacce ake karar.
“Ba na son cigaba da auren domin ba na son in yi wa Allah rashin biyayya,” in ji Murjanatu.
Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Satumba domin Murjanatu ta gabatar da shaidunta kan lamarin.