ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Soma Shari’ar Matashin Da Ya Yi Sanadin Yanke Kafar Wata Yarinya A Sakkwato 

by Sadiq
4 years ago
Shari'a

Al’umma dai sun zura ido su ga yadda zata kaya a shari’ar da aka fara ta wani matashi dan shekara 18 mai suna Aliyu Sanusi Umar, wanda ya yi sanadin yanke kafar wata yarinya daliba ‘yar shekara 16 Fatima Sulaiman a Jihar Sakkwato.

Shari’ar dai ta dauki hankalin jama’a sobada ana ganin kamar ana sako-sako da lamarin, musamman duba da fitowar da aka yi kotu a baya wanda ba a yi zaman shari’ar ba.

  • Magidanci Ya Nemi Matarsa Ta Biya Naira Miliyan 1.6 Kafin Ya Sake Ta A Kaduna
  • Shugaba Xi Ya Ba Da Umarnin Ba Da Fifiko Ga Ceton Rayuka A Gundumar Luding Da Girgizar Kasa Ta Aukawa

Labarin Fatima Sulaiman daliba ‘yar shekara 16 da ta rasa kafarta sanadiyyar bige ta da mota da Aliyu Sanusi Umar ya yi, lokacin da suke murnar kammala jarabawar NECO, ba bakon abu bane ga duk mai amfani da kafafen sada zumunta ko kafafen watsa labarai.

ADVERTISEMENT

Fatima Sulaiman, ta ce yaron ba dan makarantar su bane kuma daga farko sai da aka kore shi da ya shigo makarantar inda daliban ke wasan murnar kammala jarabawa.

Ta ce bayan an tashi makarantar sun fito waje sai yaran da ke wasan suka dauko motoci suna wasa.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

A cewarta su kuma suna zaune su uku suna jiran a zo daukar su sai motar ta nufo wurin da suke zaune, biyu daga cikin daliban da ke zaune suka gudu ita ma ta yunkura ta gudu sai ta fadi motar ta murkushe ta, ta ce tana neman a yi mata adalci ga halin da ta samu kanta ciki.

Bayan da jama’a suka yi ta yada hotonan wata fitowa kotun da aka gurfanar da yaron wadanda suke cike da shakku, yanzu dai kotun ta zauna cikin tsattsauran tsaro, inda aka tuhumi yaron da laifuka uku da suka hada da tukin mota ba tare da lasisi ba, tukin ganganci da kuma yin sanadin samuwar mummunan rauni.

A zaman kotun dai lauya mai kare wanda ake zargi, Jacob Ochidi SAN, ya nemi bukatar bayar da yaron beli domin a cewarsa laifukan da ake tuhumarsa ba manyan laifukan da ba a bayar beli ba ne.

“Doka ta ce ana bayar da beli ga laifukan da ba manyan laifuka sai in akwai wasu kwararan dalilai na kin bayar da shi, to a wannan shara’ar babu dalilan da kan iya hana a bayar da shi beli, muna tausaya wa yarinyar da iyayenta a kan yanayin da suka shiga, dukanmu ‘yan Adam muke abin da ya faru abin tausayi ne don haka muke tausaya wa iyayenta”

Sai dai lauyan masu shigar da kara, Jamilu Malami, ya kalubalanci wannan bukatar.

Ya ce, “lauyoyin yaron sun shigar da bukatar beli amma dai bangaren gwamnati da bangaren yarinyar sun ki aminta, domin sun samu wani bayanin sirri cewa yaron ya samu gurbin karatu a kasar waje don haka akwai yiwuwar zai iya barin kasar nan kowane lokaci, sannan kuma akwai yiwuwar cewa ko don lafiyar shi ya kamata a bar shi gidan gyaran hali har kura ta kwanta.”

Alkalin kotun majistire, Mariya Haruna Dogon Daji, ta dage zaman zuwa 8 ga wannan wata don yanke hukunci a kan bayar da belin ko akasin haka.

Mutane da dama na ganin dacewar hukunta yaron don zama izina ga na baya masu irin wannam dabi’a tasa ta wasa da mota.

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Mutane 8 Sun Mutu A Ruwa A Jihar Jigawa

Mutane 8 Sun Mutu A Ruwa A Jihar Jigawa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.