Taron hasalallun gwamnonin PDP biyar masu neman a cire Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, ya samu tangarɗa.
Taron wanda aka gudanar a ofishin tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Olabode George a Ikeja, ya samu halartar dukkan gwamnoni biyar masu adawa da shugabancin Iyorchia Ayu.
Rashin amincewar su da Ayu ne ya kai su ga ƙaurace wa rangadin neman zaɓen shugaban ƙasa da Atiku Abubakar ya fara.
Gwamnonin biyar sun haɗa da Nyesom Wike na Ribas, Samuel Ortom na Bennwai, Seyi Makinde na Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Okezie Ikpeazu na Abiya.
A ranar Litinin ce su ka yi sanarwar kafa ƙungiyar G5, kuma su ka kira ta da ‘Integrity Group’, wadda su ka kafa da niyyar “saita PDP kan turbar yin adalci”, a cewar su.
Sai dai kuma wasu gungun magoya bayan Atiku Abubakar da PDP sun hana taron gwamnonin biyar masu adawa da takarar Atiku yin armashi.
A wurin taron dai magoya bayan ɗan takarar sun riƙa rera take da kirarin Atiku! Atiku! Atiku! Haka su ka riƙa furtawa da ƙarfi, daidai lokacin da George ya fara bayanin cewa ba za su yi zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnonin PDP ba, amma za su yi zaɓen ‘yan majalisar dattawa da na majalisar wakilai ta ƙasa.
Mambobin PDP na jihar Legas sun halarci taron, saboda sun gano akwai maƙarƙashiyar da ake zargin Bode George ya shirya, domin ya karya lagon Atiku.
Ɗaya daga cikin mambobin PDP a Legas mai suna Kunle Folorunsho, ya saki wani bidiyon da ke tabbatar da cewa ya halarci taron, kuma akwai hayaniyar da ta kaure wurin taron duk a cikin gajeren bidiyon.
Ya ce yayin da George ya ke cikin bayanin cewa su ba za su zaɓi Atiku ba, nan da nan sai shi kuma ya miƙe tsaye ya ƙalubalance shi cewa ai PDP ta na da ɗan takarar ta Atiku Abubakar, kuma shi za su zaɓa.
Folorunsho ya ce tun bai gama rufe baki ba sai magoya bayan George su ka dira kan sa, su ka kekketa masa riga. “Da kyar wasu magoya bayan Atiku su ka cece ni daga hannun magoya bayan Bode George,” inji shi.
Yayin da gwamnonin ke shirin fita daga ɗakin taro, Folorunsho ya ce dandazon jama’ar da ke waje ba su samu shiga ba sun riƙa rera “sai Atiku, sai Atiku, sai Atiku.”
Hakan da aka yi a cewar Folorunsho ya nuna hasalallun gwamnonin biyar ba za su iya raba kawunan ‘yan PDP a jihar Legas ba.
Gwamnonin biyar masu kiran kan su G5 su da sauran hasalallun magoya bayan su, sun shafe sama da awa uku, su na tattauna matakin da za su ɗauka a gaba.
Tsohon gwamnan Filato Jonah Jang ne ya yi magana a madadin sauran gwamnonin, kuma ya ce har yanzu su na kan matsayar da su ka cimma a taron su na Fatakwal, inda su ka ce “ƙofar yin zaman sulhu da mu a buɗe ta ke.”
Sauran waɗanda su ka halarci taron na Legas kuma masu goyon bayan G5 har da Sanata Olaka Nwogu, Sanata Ohuabuwa, Sanata Nazifi Suleiman, Bello Adoke, Segun Mimiko, Ayo Fayose, Donald Duke da sauran su.