Wata ƙungiyar magoya bayan FC Barcelona mai suna ‘Sun Um Clam’ ta bukaci shugaban ƙungiyar Joan Laporta akan yayi murabus daga kan muƙamin nashi na shugabancin ƙungiyar bayan abinda suka kira gazawa da yayi wajen yin rajistar sabbin yan wasa.
A lokacin bazara Barcelona ta dauko ɗan wasan gaban kasar Sifaniya Dani Olmo dag kungiyar RB Leibzig ta kasar Jamus amma tun wancan lokacin ƙungiyar ta kasa yi mashi rajista a matsayin cikakken dan
- Anya Barcelona Za Ta Iya Kai Bantenta Kuwa A Gasar Zakarun Turai Ta Bana?
- Amurka Ta Ja Kunnen Matafiya Ƙasashe Bakwai A Afrika kwallonta,hakan ne yasa wasu ke ganin wannan a matsayin gazawa daga shugaba Joan Laporta.
Laporta ya maye gurbin tsohon shugaban Barcelona Joseph Maria Bortemeau, inda kuma yayi alkawarin dawo da martabar kungiyar ta hanyar lashe manyan kofuna, sabunta filin wasa da kuma dauko manyan yan wasa zuwa Camp Nou.
Amma tun bayan zuwansa an samu karancin rajistar manyan yan wasa,wanda daga ciki akwai Dani Olmo da Pau Victor wadanda a yanzu hak suke da yiwuwar barin Barcelona matukar ba a dauki mataki akan hakan ba.