Akalla mutane biyar ne ake zargin wasu mahara da ba a san ko su wane ba sun harbe su yayin da suka halarci wani taro a Okporo, Karamar Hukumar Orlu ta jihar Imo, a ranar Alhamis.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Micheal Abattam, ne ya tabbatar da hakan ga Asabar ga manema labarai a Owerri.
- Sama Da Mutum 500 Sun Karbi Tallafin Dogaro Da Kai A Jihar Jigawa
- Machina Ya Yi Barazanar Daukar Matakin Shari’a Kan Sauya Sunansa Da Ahmad Lawan
A cewarsa, “Suna cikin gudanar da wani taro ne maharan suka bude musu wuta.”
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar, ba ta bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu da wadanda suka ji rauni ba.
Amma wani bidiyo ya nuna yadda mutane akalla biyar da suka jikkata, wasu daga cikinsu sun samu rauni a kafa da hannu yayin da suke kukan neman agaji.
Har wa yau, kimanin mutane biyar ne aka hange su cikin jini wanda ake zargin tuni rai ya yi halinsa.
A cikin bidiyon an sake hangar wata mata tana kuka tana kiran a kai danta asibiti don ba shi agaji.
Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da sun fito cikin jini, wasu kuma dauke da raunukan harbi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp