Abokai, yau na zana wani layin dogo da ake kira “Layin dogo na Qinghai-Tibet” wanda ya hada birnin Xining na lardin Qinghai da birnin Lhasa na yankin Tibet.
An shimfida layin ne a tudun dake da matsakaicin tsayi mita 4000 daga leburin teku, hakan ya sa ya zama layin dogo mafi tsayi a duniya.
Tudun Qinghai-Tibet na da nisa matuka da teku, saboda matukar tsayi, aikin shimfida layin dogo ko hanya a wurin, na fuskantar matukar wahala.
Ya zuwa shekarar 1949, hanyar mota mai tsawon kimanin mita 1000 ne kawai yankin ke da su, baya ga kuma kwale-kwale da kuma layin jigila mai kama da lilu aka yi amfani da su.
A cikin shekaru da dama da suka gabata, saboda karancin hanyoyi da layin dogo, yankin ya fuskanci koma gaba matuka.
Shahararren mai yawon shakatawa ta jirgin kasa dan kasar Amurka Paul Theroux ya rubuta a cikin littafinsa cewa, “Ba zai yiwu a shimfida layin dogo zuwa Lahsa ba saboda tsaunin Kunlun yana da tsayi.” Amma duk da mawuyacin hali na wannan yanki, gwamnatin Sin ta lashi takobin gina layin dogo don amfanawa jama’ar dake kan wannan tudu.
Daga shekarar 1958 zuwa 2006, gwamnatin Sin ta daidaita kalubalolin da aka fuskanta wajen gina layin dogon sakamakon duwatsu masu tsayi da daskarewar kasa da kare muhalli da sauransu, inda ta shafe shekaru 48 tana aikin gina layin dogo na Qinghai-Tibet, mai tsawo kilomita 1956 dake da tasoshi 85.
Ya zuwa karshen watan Yuni na bana, an yi jigilar fasinjoji kimanin miliyan 260 ta wannan layi, daga cikinsu masu yawon shakatawa dake shiga ko fito yankin Tibet ya kai fiye da miliyan 31.
Ban da wannan kuma, a watan Yuli na bana, an fara aikin inganta tashar Delingha, matakin da ya daga matsayin mu’amula tsakanin yankin da sauran sassan kasar da ma kyautata zaman rayuwar jama’ar wurin.
Jama’ar kabilar Zang sun yabawa wannan layin dogo, ta hanyar rera wata waka cewa, “Muna matukar maraba da wannan layin, wanda ya hada mu da sauran wurare. Wannan layi mai muhimmanci ya samar da zaman rayuwa mai kyau da alheri da wadata……”
Layin dogo na Qinghai-Tibet na da babbar ma’ana wajen kawar da talauci a yankin Tibet da ingiza mu’ammala tsakanin kabilu daban-daban na kasar da tabbatar da samun wadata tare a tsakaninsu, da ma ingiza bunkasuwar tattalin arziki da bunkasuwar al’ummar lardin Qinghai da jihar Tibet.
Shimfida layin dogo a wannan yanki, wanda a baya wasu ke ganin ba zai taba yiwuwa ba, a halin yanzu gwamnatin Sin ta yi nasarar kammala shi.
Aikin da ya zama abin mamaki a tarihin gina layin dogo a duniya, kuma ya bayyana manufar gwamnatin Sin ta bautawa jama’a da mai da jama’a a gaban kome. (Mai zane da rubuta: MINA)