Wasu rahotannin kafofin watsa labaru na cewa, wai kasar Italiya tana tunanin jinkirta sanya hannu kan muhimman takardun da suka shafi shawarar ziri daya da hannu daya. Sai dai ana fatan hakan ba zai shafi dangantakar Italiya da Sin ba, kuma Italiyar na son ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin. Ana tambaya, shin menene martanin kasar Sin kan wannan batu?
Da yake amsa wannan tambaya, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, yadda Sin da Italiya ke raya shawarar ziri daya da hanya daya, zabi ne da ya dace da kasashen biyu suka yi, bisa tushen tarihi da al’adu da bukatun ci gaba a zahiri. Kana sanya hannu kan takardar hadin gwiwar shawarar ya kara zaburar da damar yin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu. Kana cikin shekaru biyar da suka gabata, darajar cinikayya tsakanin kasashen biyu, ta karu da kashi 42 cikin 100, inda ya kai kusan dalar Amurka biliyan 80 a bara.
Ya ce wasu makiya daga waje, suna ci gaba da yin katsalandan wajen neman siyasantar da hadin gwiwar al’adu da tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin Italiy a fannin gina shawarar ziri daya da hanya daya tare, inda suke katsalandan ga hadin gwiwar, da haifar da rarrabuwar kawuna, wannan ya saba wa tsarin tarihi, kuma hakan suna cutar da wasu ne ba kuma tare da amfanar da kansu ba.(Ibrahim)