A yayin da tattalin arzikin duniya ke cikin halin rashin tabbas a sakamakon tarin matsalolin da suka yi masa dabaibayi, hakika, tattalin arzikin duniya yana fama da wahalhalu a wannan lokaci.
Koda yake, mai yiwuwa ne tattalin arzikin duniyar zai iya samun sassauci gami da farfadowa a sakamakon wasu jerin matakan da kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya ke dauka, wadanda suka shafi matakan daidaita yanayin tattalin arzikin kasar na cikin gida kuma ka iya yin tasiri ga bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.
A karshen wannan mako ne, babban bankin duniya ya fitar da sabon rahoto kan tattalin arzikin kasar Sin, inda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi tsokaci kan wannan batu, inda ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar kalubale daban-daban a cikin gida da kuma waje, tattalin arzikin kasar Sin zai iya tabbatar da daidaito da samun ci gaba na dogon lokaci da ma ba da kwarin gwiwar daidaitawa da farfado da tattalin arzikin duniya.
Sabon rahoton tattalin arzikin Sin din da babban bankin duniya ya fitar ya nuna cewa, a cikin rubu’in farko na wannan shekara, tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasa sosai. Biyo bayan wasu tsare-tsare da matakai na daidaita tattalin arziki, ana sa ran saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya sake dawowa a cikin rubu’i na biyu na wannan shekara.
Ita ma babbar hukumar kwastom ta kasar Sin GAC, ta sanar da cewa, a watanni biyar din farko na shekarar 2022, hada-hadar cinikayyar kasashen waje na kasar Sin ya samu karin kashi 8.3 bisa 100, idan an kwatanta da makamancin lokacin bara inda adadin ya karu zuwa RMB yuan triliyan 16.04. Ta fannin dalar Amurka kuwa, jimillar cinikayyar kasashen wajen ya kai dala triliyan 2.51 a cikin watannin biyar, inda ya karu da kashi 10.3 a bisa na makamancin lokacin bara.
A cikin wannan wa’adi kuma, cinikayyar kasar Sin da manyan abokan huldar kasuwanci uku, wato kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, da kungiyar tarayyar Turai, da kuma Amurka, ya karu da kashi 8.1 bisa 100, da kashi 7 bisa 100, da kuma kashi 10.1 bisa 100, idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.
Daga watan Janairu zuwa Mayu, huldar kasuwancin Sin da kasashen dake bin shawarar “ziri daya da hanya daya”, ya karu zuwa kashi 16.8 bisa 100 a bisa na makamancin lokacin bara, inda ya karu zuwa RMB yuan triliyan 5.11. Abin da ya bayyana a fili shi ne, an samu farfadowar ne bayan da gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan tallafawa kamfanonin kasashen ketare, wajen rage musu wahalhalu a sakamakon barkewar annobar COVID-19 a cikin gida, da kuma rashin tabbas a yanayin tattalin arzikin kasashen ketare.
A cewar Li Kuiwen, jami’in babbar hukumar GAC, kasar Sin ta bullo da wasu jerin matakan daidaita yanayin tattalin arziki, da kuma inganta yanayin kasuwancin waje a cikin wannan shekarar, matakan wadanda dama an yi tsammanin za su taimaka wajen saurin farfadowar tattalin arzikin da zarar suka fara aiki.
Ko shakka babu, wadannan wasu alamu ne a bayyane dake kara nuna tasirin matakan da kasar Sin ke dauka wajen daidaita yanayin tattalin arzikinta wadanda ba kawai suna amfanawa kasar kadai ba ne, har ma suna kara samar da tabbaci ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Ahmad Fagam)