A yau shafin namu zai kawo wasu abubuwa ne guda 21 da ya kamata magidanta su rika yi wa ‘ya`yansu mata huduba da su domin fadakarwa a kan zamantakewar rayuwa.
1: Ka fada wa ‘yarka cewa shi kudi ba ruwansa da ko kai wane ne, za ta iya samun kudi kamar yadda kowane mutum zai iya samu watakila ma ta fi shi.
2: Ka fada mata ta fita nema amma ba ta kasance a gado ba domin ta samu kudi, saboda kudin da za a samu ta hanyar fita domin yin fafutukar wani aiki akwai martaba, su kuma kudin da za a samu kan gado kada ta manta da cutar ciwon sanyi da akan dauka ta waccan hanyar.
3: Fada wa ‘yarka ta yi amfani da kwakwalwarta ba wai al’aurarta ba domin ta samu kudi.
4: Ka horar da ‘yarka kar ta yi addu’a domin ta auri mai arziki, amma ta yi addu’ar da zata sa ta zama mai arziki.
5: Hori ‘yarka kada tayi addu’a domin ta auri gwamna amma ta yi addu’a domin ta zama Shugaban kasa.
6: Fada wa ‘yarka cewar sai an sha wuya ake shan dadi ba a tsaya ba yin wani abu ba ana wuri daya, a maida hankali ga yin maula.
7: Fada wa’yarka kada ta maida hankalinta kan wan mutum amma ta maida hankalinta ta yadda watarana wasu mazan za su rika maganarta.
8: Fada wa’yarka cewa ba wani mutum da za so ta kamar yadda Allah ke son ta don haka kada ta yi wasa wajen abubuwan da za su sa ta kara samun yarda wurin mahaliccinta.
9: Fada wa ‘yarka ita kafar sadarwa bata mantuwa bare yafewa don haka irin rubutu mara fa’ida da za ta yi akan kafar sadarwar na iya bata mata rayuwa a gaba.
10: Fada wa ‘yarka lokaci baya jiran mutum don haka idan ta bata wa lokacinta wajen yin tarayya da wawan mutum daga karshe zata gane ashe kanta ne ta bata wa lokaci.
11: Fada wa ‘yarka abin da mutum ya shuka shine ai girba rashin shuka alheri babbar matsala ce a gaba.