Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu na Ko Kin San.
Saiwar zogale tana da amfani sosai a jikin mace tana gyara mace tana dawo miki da martabarki.
- Kafar Sadarwa Ta Karrama Fintiri, Bindow, Boss Mustapha Da Wasu 17 A Adamawa
- Gobara Ta Lalata Shaguna 10 A Adamawa
Za ki samu saiwar zogale da tafarnuwa sai ki wanke ta ki zuba a tukunya tare da tafarnuwar sai ki tafasa su tafasu sosai sannan ki sauke ki barshi ya sha iska sai ki zauna a ciki kamar minti sha biyar zuwa ashiri haka.
Sai kuma amfanin Abarba:
Abarba tana da amfani sosai lokacin da mace take jin kasala ba za ta iya yin jima’i ba.
To ki samu abarba ki yanka ta ki yi ta sha.
Sannan kuma idan shima maigida yanajin wannan kasalar shima za ki iya bashi ya sha.
Yawan shan Abarba yana canza maniyi ya zama mai kamshin dadi kamar alawa haka.
Kema uwargida idan kina yawan shan Abarba gabanki zai rika fitar da kamshi mai dadi.