Maiyaki (Estu) na Kupa, Alhaji Mohammadu Kabir Isah (II), sarkin Kupa ya rasu bayan ya kwashe sama da shekaru 42 akan karagar mulki.
Ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Bida, babban birnin jihar Neja ranar Lahadi.
Marigayi sarki ya zama sarkin gargajiya na kasar Kupa a ranar 2 ga Oktoba, 1979.
Har zuwa rasuwarsa, ya kasance mataimakin shugaban majalisar gargajiya ta Lokoja kuma mai Sanya ido da lura kan al’adun kasar Kupa.
Marigayin, sarki ne da ake girmamawa matuka a kasar Nufawa kuma babban mashawarci ne ga Sarkin Bida, Etsu Nupe.
Sarki Alhaji Muhammadu Kabiru Issa (II) yana cikin sarakunan gargajiya da aka daga darajarsu zuwa matakin farko shekaru uku da suka gabata.
Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya da jikoki da tattaba-kunne. Daga cikinsu akwai Ambasada Adamu Isa da Dauda Kabir Isa, masanin kimiyyar harhada magunguna; Malam Umar Kabir Isa, Hauwa Isa, Hajara Isa da Malam Abdulmalik Suleiman.
An yi jana’izarsa a garin Abugi Kupa da ke karamar hukumar Lokoja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.