Sakamakon dambawar zaben kananan hukumomin Neja da majalisar dokokin jiha ta shelanta dakatar da shugaban hukumar zabe ta jiha, Alhaji Baba Aminu.
Shugaban kungiyar lauyoyin jihar, Mohammed Waziri Abdulkadir ya bayyana cewar majalisar ta yi hawan kawara ga dokar zabe ta jiha sashi na 201 da 197 na shekarar 1999 da aka yiwa gyaran fuska, dan haka ya nemi majalisar ta canja tunanin ta.
- Manchester United Ta Kafa Mummunan Tarihi A Watannin Oktoba
- Yadda Ake Tabbatar Da Ci Gaba Mai Inganci A Birnin Shanghai Na Kasar Sin
Majalisar ta bayyana dakatar da shugaban hukumar zabe ta jiha inda suka zarge shi da rashin cancantar shugabantar hukumar NISIEC.
Alh. Baba Aminu ya halarci majalisar a wani gayyatar da tai mai saboda maganar ci gaba da shirye-shiryen zaben kananan hukumomi da hukumar ke aiwatarwa a halin yanzu inda majalisar ta nemi a dakatar da zaben wanda za a gudanar a watan Nuwambar wannan shekarar.
Hukumar NISIEC na shirya zaben ne sakamakon wa’adin shugabannin kananan hukumomi zai kare watanni uku masu zuwa, kuma majalisar ta nemi a dakatar da shirya zaben sakamakon karar rashin amincewar zaben da jam’iyyar PDP ta shirgar a babban kotun tarayya da ke minna nakin amincewa da zaben a halin yanzu.
Sakamakon tambayoyin manema labarai ga shugaban kungiyar lauyoyin jiha, Mohammed Waziri Abdulkakir ya bayyana cewar majalisar bata da hurumin dakatar da shugaban hukumar zaben, domin dakatarwar ya sabawa doka kuma bai kan ka’idar doka.
“Ba su da hurumin dakatar shugaban hukumar zabe, gwamna ne kawai ke da hurumin neman tsige shugaban ko dakatarwar, sannana samu kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar su amince da hakan”.
Yanzu labaran da muke samu awani zaman majalisar wanda gefe daya ne suka zartas da hukuncin.
Kora ko dakatarwar na majalisar ya fito ne daga gwamna ko majalisar dokokin ne tai gaban kan ta na dakatarwar.
Lauyan ya shawarci majalisar da su bi dokar da ta samar da hukumar da kuma bai wa hukumar shugabanci da sakataren hukumar da sauran manyan masu mukamai a hukumar, ya jawo hankalin majalisar akan dokar 1999 da ta samar da hukumar.
“Bari in sake tambaya, shin dakatarwar daga majalisar ne, domin ba wanda ke da hurumin dakatarwa ko korar shugaban hukumar zabe da sakataren hukumar sai gwamna.
Sashi na 201 ya bayyana cewar sai kashi biyu bisa uku na majalisar ta amince da kudurin, yanzu abin da wannan ke magana gwamna ne yake da hurumin neman majalisar dokokin da ta cire shugaban hukumar”.
Saboda haka abinda dokar ya ce, maganar korar shugaban hukumar zabe gwamna kawai ke da wannan damar, ina kira ga majalisar dokokin da su canja tunanin su akan korar shugaban hukumar zabe.
Abdulkadir ya bayyana cewar a zaman kungiyar na gaba za ta tattauna wannan batu dan samar da matsayar doka, dan nuna matsayin su akan irin wannan matsalar saboda gaba.
Tunda farko shugaban majalisar dokokin jiha, Barista Abdullahi Bawa Wuse ya nemi gwamnatin jiha da hukumar zaben su dakatar da batun zaben har sai bayan kamala shari’ar da ke gaban kotu kan yiwuwar gudanar da zaben, wanda gwamnati da hukumar ke cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaben.
Kungiyar jam’iyyun siyasa da ke jihar ( IPAC) bisa jagorancin Hon. Bello Maikujeri ta bayyana gamsuwar takan matsayin hukumar na gudanar da zaben kamar yadda shirye-shiryen ke gudana a halin yanzu.
A wani karin hasken da ya yi wa manema labarai, ya ce sanin kowa ne shugabannin kananan hukumomi na yin shekaru biyu ne a sake zabe, amma saboda sabon dokar da majalisar dokokin jiha suka yi, ya bai wa kananan hukumomi damar wa’adin shekaru uku, yanzu wa’adin su zai kare cikin watan Disamba, ka ga ke dole ne a yi zabe tun da sabon dokar ya ce ba rikon kwarya, in ban da PDP dukkanin jam’iyyun siyasar har APC mai Mulki sun amince da maganar zaben.
Saboda wannan dambarwar da majalisa ke son kawo wa son zuciya kawai amma ba maganar ci gaban dimukuradiyya ba.
Kamar yadda hukumar zaben ta ba mu damar ci gaba da shirye-shirye mafi yawan jam’iyyu sun kammala zaben fidda gwani kuma a shirye muke don fara yakin neman zabe kamar yadda aka tsara.
Wasu rahotanni dai sun tabbatar da cewar gwamnati ta sanya kwamiti don nazartar sabon dokar da kuma yiwuwar yin zaben ko rashin sa.
Tsoron da jama’a ke yi kan zaben yana da nasaba da babban zaben kasa na shekarar 2023 mai da ake zargin idan zaben ya gudana yana iya kara barazana da fargaba a samun babban zaben mai zuwa.