Kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati ya ba da wa’adin sa’o’i 24 ga babban jami’i (GCEO) na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, da ya gurfana a gabanta ko kuma ya fuskanci sammacin kama shi kan kin amsa gayyatar da aka yi masa na neman amsa wasu tambayoyi.
Shugaban kwamitin, Aliyu Wadada, ya bayar da wannan umarni a zaman da wakilan kamfanin na NNPC a zauren majalisar dokokin kasar, inda ya yi gargadin cewa majalisar dattawa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da karfin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba ta idan Ojulari ya gaza yin hakan.
- Hukumar ‘Yansanda Ta Yi Wa Wasu Manyan Jami’anta Karin Girma
- Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi
Ojulari, wanda a yanzu ya kasa amsa gayyata guda hudu, maimakon haka ya aika da babban jami’in kula da harkokin kudi, Dapo Segun, domin ya wakilce shi, matakin da ya harzuka ‘yan kwamitin da suka dage cewa bayyanar ba ta wadatar ba.
Segun, wanda ya bayyana a gaban kwamitin, ya ce Ojulari bai halarci taron ba saboda gayyatar da shugaban kasa ya yi masa ba zato ba tsammani. A cewar wata wasika mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Yuli, wanda magatakardar kwamitin, Mohammed Sani Abdullahi, ya karanta a bayyane, Shugaban Kasa Bola Tinubu ne ya gayyaci GCEO da misalin karfe 1 na rana, wanda hakan ya hana bayyanarsa.
Sai dai Sanatoci sun yi watsi da bayanin, inda suka zargi Ojulari da yin watsi da Majalisar. Kwamitin yana binciken tambayoyin tantancewa daga shekarar 2017 zuwa 2023, wanda ya nuna sabanin da ya kai Naira tiriliyan 210, ciki har da bashin da ba a tabbatar da shi ba na Naira tiriliyan 103. ‘Yan majalisar sun firgita cewa Naira tiriliyan 3 zuwa 5 ne kawai aka rubuta a cikin asusun ribar da kamfanin ya samu a cikin shekaru shida.
“Wannan gayyatar ba tilas bace,” in ji Wadada. Ya kara da cewa kwamitin ba yana zargin hukumar ta NNPC da laifin sata bane amma ya jaddada cewa girman sabanin ya bukaci a yi karin haske kai tsaye. Ya bayyana rashin bayyanar Ojulari a matsayin “Cin mutunci” ga kwamitin da ‘yan Nijeriya, ya kara da cewa amincewa da jama’a ga NNPCL ya dogara ne akan gaskiya.
‘Yan majalisar sun bayyana bacin ransu kan rashin zuwan GCEO akai-akai. Sanata Bictor Umeh ya yarda cewa kiran shugaban kasa na iya tabbatar da rashin zuwan Ojulari na baya-bayan nan amma ya yi gargadi game da amfani da Shugaba Tinubu a matsayin garkuwa daga bin doka da oda. “Kada a bar wannan uzurin ya ci gaba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp