Majalisar dattawa ta yi fatali da yunkurin daukar matakin amfani da karfin soji a kan Jamhuriyar Nijar.
Majalisar ta yi kira ga mambobin ECOWAS da sauran shugabanni da su yi tir da juyin mulki a kasar tare da tashi tsaye wajen daidaita lamura ta sigar da ya dace.
- Bukatar Rogo A Duk Shekara A Nijeriya Ya Kai Tan Miliyan 300,000, Cewar Masana
- Manchester United Ta Dauki Hujland Daga Atalanta
A cewar majalisar akwai bukatar daukar matakan laluma da zurfin tunani wajen shawo kan rigimar shugabanci da ke faruwa a Nijar.
A ranar Juma’a ne shugaba Tinubu ya rubuta wasika ga majalisar ya a neman amincewarta kan aiwatar da matsayar da shugabanni ECOWAS suka cimma a kan halin da kasar Nijar ke ciki.
A jawabin ECOWAS da shugabanta, Bola Ahmed Tinubu ya fitar, ya ce daukar matakin karfin soji ne kawai zai kawo karshen juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.
A yayin zaman majalisar a ranar Asabar, Sanata Bamidele Opeyemi, ya bijiro da batun tare da nuna adawa da matakin karfin Soja, inda majalisar ta cimma matsayar kin amincewa da matakin tare da neman shugaban Nijeriya da ya kara azama wajen ganin an shawo kan rikicin ta hanyar tattaunawa.
Da yake magana bayan zaman da majalisar ta yi a sirrance na tsawon awa biyu, shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya ce ba su amince a dauki matakin Soja kan Nijar ba ne saboda kyakkyawar alaka da ta jima a tsakanin Nijar da Nijeriya.
“Zaman namu, majalisa ta yi tir da juyin mulkin da ya wakana a jamhuriyyar Nijar.
“Majalisa ta jinjina wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni ECOWAS bisa daukan matakin gaggawa kan lamarin.”
Ya ce, amma Tinubu ya bi matakin tambayar majalisar domin zuwa ga fagen yaki domin aiwatar da matsayar da ECOWAS ta cimma, “Jagorancin majalisa za ta samu shugaban kasan domin fadi masa matakin da ya dace a dauka domin shawo kan wannan lamarin domin tabbatar ba a lalata alakar da ke tsakanin Nijar da Nijariya ba,” Akpabio ya shaida.