• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisa Ta Soki Zaben Kananan Hukumomi A Matsayin Cin Fuska Ga Dimokuradiyya

by Yusuf Shuaibu
11 months ago
Majalisa

Majalisar wakilai ta soki yadda gwamnatocin jihohi ke gudanar da zaben kananan hukumomi, inda ta bayyana shi a matsayin cin fuska ga dimokuradiyya.

A cewarsu, wannan lamari ya gurgunta ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi, kuma dole ne a magance lamarin domin a kiyaye ka’idojin dimokuradiyya.

  • Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-wadai Da Rufe Fadar Sarkin Kano 
  • Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Waɗanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen ya bayyana hakan ne a jawabinsa na bude taron tattaunawa kan gyara zaben kananan hukumomi da tsarin mulki na kasa, wanda kwamitin majalisar kan duba kundin tsarin mulki ya shirya a ranar Litinin da ta gabata a Abuja.

Tajuddeen ya ce, “Lokacin da zabubbuka suka kasance mara tsari, inda jam’iyya mai mulki ta mamaye dukkan mukamai, ya bayyana a fili muna cewa wanna cin fuska ne ga ka’idojin dimokuradiyya,” in ji Tajuddeen. Ya kara da cewa irin wadannan zabukan ba wai kawai na kawo cikas ga dimokuradiyya ba ne, har ma suna haifar da matukar damuwa game da daidaito da ayyukan kananan hukumomin.

“Wannan yanayin ba abin kunya ba ne kawai, yana kawo babbar barazana ga dimokuradiyyarmu. Yana haifar da mummunn yanayi, inda abubuwan da ba a so suke kutsawa cikin kananan hukumomi, galibi ba su da karfin da ake bukata da hangen nesa don gudanar da mulki yadda ya kamata.

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

“Saboda haka, kananan hukumomi sun zama ‘yan amshin shatan gwamnatocin jihohi ko kuma ‘yan amshin shata a hannun ubangidan siyasa wadanda ke yin magudin zabe domin samun riban kashin kai,” in ji shi.

Tajuddeen ya bayyana rashin isassun kudade a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da kananan hukumomi ke fuskanta. “Yawancin gwamnatocin kananan hukumomi suna aiki da kasafin kudin da bai isa ya sauke nauyin da ke kansu ba,” in ji shi.

Ya kuma jaddada batun ‘yancin cin gashin kai, inda ya ce gwamnatocin jihohi ne ke sarrafa kananan hukumomi, wanda hakan ke haifar da tsoma baki wajen yanke shawara. A cewarsa, wannan rashin ‘yancin kai ne kuma yana dakushe romon dimokuradiyya a matakin kananan hukumomi.

Rashin isassun iya aiki daga fannin albarkatun Dan’adam da tsare-tsaren hukumomi ya kuma kawo cikas ga ingantaccen shugabanci a matakin kananan hukumomi. Yawancin ma’aikatan kananan hukumomi ba su da horo da kwarewa da ake bukata don gudanar da ingantaccen aiki, wanda hakan ke shafar samar da ayyuka da kuma sauke nauyin al’umma wajen gudanar da mulkin kananan hukumomi.

A halin da ake ciki, mataimakin shugban majalisar wakilai, Benjamin Okezie Kalu, wanda shi ne ya shugaban kwamitin majalisar kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, ya jaddada bukatar hada karfi da karfe a tsakanin masu ruwa da tsaki domin samun gyara mai ma’ana a harkokin kananan hukumomin Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Next Post
Guguwa Mai Ƙarfi Ta Sa An Soke Wasan Liverpool Da Everton Na Yau

Guguwa Mai Ƙarfi Ta Sa An Soke Wasan Liverpool Da Everton Na Yau

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.