Majalisar dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
Majalisar ta kuma tabbatar da Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren EFCC da Halima Shehu a matsayin shugabar hukumar kula da zuba jari ta kasa (NSIPA).
- Xi Ya Gana Da Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya
- GDPn Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5.2% A Farkon Watanni 9 Na Shekarar 2023
An tabbatar da wadanda aka nada bayan an tantance su a gaban majalisa a ranar Laraba.
An yi musu tambayoyi da dama da kuma batutuwa kan dalilin da ya sa shugaba Tinubu ya nada su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp