A jiya Talata, Majalisar Dattijai ta yi watsi da ƙarar cin zarafi da aka shigar kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wacce Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, da aka dakatar ta shigar.
Mai shigar da ƙarar, Zuberu Yakubu, wanda ke wakiltar Sanata Akpoti-Uduaghan, ya zargi Kwamitin Ladabtarwa da Ƙorafe-ƙorafe da nuna son rai saboda kin bashi damar gabatar da hujjoji yadda ya kamata.
- Wani Bawan Allah Ya Rasu Jim Kadan Bayan Sallar Asuba A Wani Masallaci A Abuja
- Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya
A yayin zaman kwamitin a jiya Talata, Yakubu ya zo tare da lauyansa, Dakta Abiola Akiyode, da tsohuwar Ministar Ilimi, Dr. Oby Ezekwesili, amma ya ƙi yin jawabi, inda ya ce, har sai an bar Sanata Akpoti-Uduaghan, babbar shedarsa, ta shiga ginin Majalisar.
A nan ne rashin jituwa ta ɓarke lokacin zaman, yayin da aka samu saɓani tsakanin Sanata Onyekachi Nwaebonyi da Ezekwesili, a lokacin ne Yakubu ya yi yunƙurin yin magana a gaban Shugaban Kwamitin, Sanata Neda Imasuen, amma rashin fahimta ya kara dagulewa tsakanin sheda, mai wakiltar Akpabio da Ezekwesili inda hakan ya sa aka gaggauta dakatar da zaman.
Bayan da aka yi watsi da ƙarar, Yakubu ya bayyana cewa, ya ƙi yin magana a gaban kwamitin ne saboda yana ganin an riga an nuna son rai, ya kuma zargi Shugaban Kwamitin, Sanata Imasuen, da yin maganganu masu nuna hukunci a kafafen watsa labarai kafin zaman.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp