Majalisar Dattawa ta bukaci Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya sake duba manufofinsa kan tsarin takaita cirar kudade.
Babban bankin a karkashin sabon tsarin cire kudi, ya takaita yawan kudaden da mutane da kamfanoni za su rika cirewa duk mako daga N100,000 zuwa N500,000.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Zai Yi Jawabi A Yayin Bude Taro Zagaye Na 2 Na Yarjejeniyar COP15
- 2023: Mallakar Katin Zabe Ya Fi Mallakar Takardun Makaranta A Wannan Lokacin -Gumi
Sai dai majalisar dattijai bayan ta yi la’akari da rahoton kwamitinta kan harkokin banki, wanda ya hada baki da shugabannin bankin CBN kan wannan manufa, ta bukaci bankin da ya daidaita ka’idojin fitar da kudi domin duba da koke-koken jama’a da ya biyo baya.
Majalisar ta kuma umarci kwamitinta da ya fara sa ido a kan babban bankin CBN kan kudirinsa na daidaita kai rahoto ga majalisar dattawa lokaci-lokaci.
Har ila yau, ta kuduri aniyar tallafa wa babban bankin a ci gaba da aiwatar da ayyukan samar da canji da kuma ayyukan masana’antu da hada-hadar kudi kamar yadda ya dace da dokar CBN.