Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya na tsawon watanni shida, daga ranar 6 ga Maris, 2025, bisa zarge-zargen rashin da’a da kuma saba dokokin majalisar dattawa (wacce aka yi wa kwaskwarima a 2023)
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, rikicin da ya kai ga dakatar da ita ya samo asali ne tun a watan Fabrairun da ya gabata lokacin da takaddamar sauya kujerar zama a zauren majalisar ta yi sanadin cacar baki tsakanin Sanata Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio. Rikicin dai ya rikide zuwa zarge-zargen rashin da’a, lamarin da ya haifar da damuwa game da tsarin majalisar. Sai dai Akpabio ya musanta aikata laifin cin zarafin Sanatar, inda ya bayyana a ranar Laraba cewa “bai taba cin zarafin wata mace ba.”
A zamanta na ranar Alhamis, kwamitin majalisar dattijai mai kula da da’a, gata, da sauraron kararrakin jama’a, karkashin jagorancin Sanata Neda Imasuen, ya gabatar da sakamakonsa, inda ya bayar da shawarwari guda bakwai. A cewar kwamitin, Akpoti-Uduaghan ta gaza bin dokokin majalisar dattawa sannan kuma ta yi watsi da kwamitin ta hanyar kin amsa gayyatar da ya yi mata.
Don haka, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda saba ka’idojinta na majalisar dattawa.
Bugu da kari, majalisar ta bukaci Natasha da ta maido da duk wani abu mallakin majalisar ga mai kula da Majalisar har sai lokacin dakatarwar ya cika.
Sanata Imasuen ya bayyana cewa, “A madadin kwamitin majalisar dattawa kan da’a, gata, da kuma sauraron kararrakin jama’a, muna godiya ga shugaban kasa da manyan abokan aikinmu bisa damar da aka ba mu na yi wa ‘yan Nijeriya hidima ta hanyar wannan kwamiti. Mun gabatar da shawarwarinmu cikin girmamawa don tantancewa da amincewa. Na gode.”
Bayan doguwar muhawara kan rahoton da kwamitin ya gabatar, Sanatocin sun amince da dukkan shawarwarin ta hanyar kada kuri’a tare da yin kwaskwarima ga shawara ta 6, inda aka bai wa mataimakan Sanata Natasha damar karbar albashi da alawus-alawus din su domin kada su tagayyara.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, dukkan Sanatocin da suka yi magana sun nuna goyon bayansu ga sakamakon binciken.
A yayin da Sanatocin suka amince da shawarwarin, Sanata Natasha ta yi tsinkaye kan zaman, inda ta ce zalincin da aka yi mata ba zai dore ba. Daga nan aka fito da ita daga dakin zauren majalisar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp